Hausa translation of the meaning Page No 413

Quran in Hausa Language - Page no 413 413

Suratul Luqman from 20 to 28


20. Ashe, ba ku gani ba, cẽwa Allah Yã hõre muku abin da ke a cikin sammai da abin da ke a cikin ƙasã, kuma Ya zuba ni'imõminsa a kanku, bayyanannu da ɓõyayyu? Kuma akwai daga mutãne wanda ke yin jidãli ga al'amarin Allah, bã da wani ilmi ba, kuma bã da wata shiriya ba, kumã ba da wani littãfi mai haskakãwa ba.
21. Kuma idan aka ce musu, « Ku bi abin da Allah ya saukar, » sai su ce: « Ã'a, munã bin abin da muka sãmi ubanninmu a kansa. » shin kõ dã Shaiɗan nã kiran su ne zuwa ga azãbar sa'ir,
22. kuma wanda ya mĩka fuskarsa zuwa ga Allah, alhãli kuma yanã mai kyautatãwa, to, lalle ya yi riƙo ga igiya amintacciya. Kuma zuwa ga Allah ãƙibar al'amura take.
23. Kuma wanda ya kãfirta, to, kada kãfircinsa ya baƙanta maka rai, zuwa gare Mu makõmarsu take, sa'an nan Mu bã su lãbari game da abin da suka aikata. Lalle Allah, Masani ne ga abin da ke a cikin ƙirãza.
24. Munã jĩshe su dãdi kaɗan sa'an nan Mu tĩlasta su ga shiga zuwa azãba kakkaura.
25. Kuma lalle, idan ka tambaye su, « Wãne ne ya halĩtta sammai da kasa? » Lalle zã su ce: « Allah ne. » Ka ce: « Gõdiya ta tabbata ga Allah » Ã'a, mafi yawansu ba su sani ba.
26. Abin da yake a cikin sammai da ƙasa duka na Allah kawai ne. Lalle, Allah Shĩ ne Mawadãci, Gõdadde.
27. Kuma dã dai abin da ke a cikin ƙasa duka, na itãce, ya zama alƙalumma, kuma tẽku tanã yi masa tawada, a bayansa da waɗansu tẽkuna bakwai kalmõmin Allah ba zã su ƙãre ba. ( 1 ) Lalle, Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
28. Halittarku bã ta zama ba, kuma tãyar da ku bai zama ba, fãce kamar rai guda. Lalle, Allah Mai jĩ ne, Mai gani.
( 1 ) Wannan bayãni ne ga yawan ilmin Allah, watau yanã nũnawa mutãne cẽwa su yi aiki da ilmin da Ya bã su, mai amfãni zuwa gare su, kada su wuce shi zuwa nẽman wani ilmi daga wani abu, su bar Allah, su halaka a kan wani ilmi da bai umurce su da su yi aiki da shi ba. Ilmin da Ya bã su a cikin Alƙur'ãni shi ne sharĩ'a wãtau hanya mai kai su ga Aljanna. Sauran hanyõyi ɓata ne.