Hausa translation of the meaning Page No 412

Quran in Hausa Language - Page no 412 412

Suratul Luqman from 12 to 19


12. Kuma lalle haƙĩƙa Mun bai wa Luƙmãn hikima. ( Muka ce masa ) Ka gõde wa Allah, kuma wanda ya gõde, to yanã gõdẽwa ne dõmin kansa kawai kuma wanda ya kãfirta, to, lalle, Allah Mawadãci ne, Gõdadde.
13. Kuma a lõkacin da Luƙmãn ya ce wa ɗansa, alhãli kuwa yanã yi masa wa'azi, « Yã ƙaramin ɗãna! Kada ka yi shirki game da Allah. Lalle shirki wani zãlunci ne mai girma. »
14. Kuma Mun yi wasiyya ga mutum game da mahaifansa biyu; uwarsa tã ɗauke shi a cikin rauni a kan wani rauni, kuma yãyensa a cikin shekaru biyu ( Muka ce masa ) « Ka gõde Mini da kuma mahaifanka biyu. Makõma zuwa gare Ni kawai take. »
15. « Kuma idan mahaifanka suka tsananta ( 1 ) maka ga ka yi shirki game da Ni, ga abin da bã ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗã'a. Kuma ka abũce su a cikin dũniya gwargwadon sharĩ'a, kuma ka bi hanyar wanda ya mayar da al'amari zuwa gare Ni, sa'an nan zuwa gare Ni makõmarku take sa'an nan In bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
16. « Yã ƙaramin ɗãna! Lalle ita idan gwargwadon ƙwãyar kõmayya ce ta kasance, to, ta kasance a cikin wani falalen dũtse, kõ a cikin sammai, kõ a cikin ƙasã, Allah zai kãwo ta Lalle Allah Mai tausasãwa ne, Masani. »
17. « Yã ƙaramin ɗãna! Ka tsai da salla, kuma ka yi umurni da abin da aka sani, kuma ka yi hani daga abin da ba a sani ba, kuma ka yi haƙuri a kan abin da ya sãme ka. Lalle, wancan yanã daga muhimman al'amura. »
18. « Kada ka karkatar da kundukukinka ( 2 ) ga mutãne, kada ka yi tafiya a cikin ƙasã kanã mai nũna fãɗin rai. Lalle, Allah bã Ya son dukan mai tãƙama, mai alfahari. »
19. « Kuma ka tsakaita a tafiyarka, kuma ka runtse ga sautinka. Lalle mafi mũnin sautuka haƙĩƙa shĩ ne sautin jãkuna. ( 3 ) »
( 1 ) A bãyan haƙƙin Allah sai haƙƙin uwãye. Sabõda haka ba zã a yi ɗã'a ga uwãye ba ga abin da ya sãɓã wa Allah.
( 2 ) Karkata kundukuki ga mutãne, alamar wulãkanta su ne.
( 3 ) A nan ne iyãkar wasiyyar Luƙmãn ga ɗansa. Sa'an nan kuma Allah Ya ci gaba da bayãnin yadda ake tarbiyyar mutãne.