Hausa translation of the meaning Page No 422

Quran in Hausa Language - Page no 422 422

Suratul Al-Ahzab from 31 to 35


31. Kuma wadda ta yi tawãli'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, zã Mu bã ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karimci.
32. Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri.
33. Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, ( 1 ) kuma kada ku yi fitar gãye- gãye irin fitar gãye- gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩ da salla, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã,ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakẽwa.
34. Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗãkunanku daga ãyõyin Allah da hukunci. Lalle Allah Yã kasance Mai tausasãwa Mai labartawa.
35. Lalle, Musulmi maza da Musulmi mãtã da muminai maza da muminai mãtã, da mãsu tawãli'u maza da mãsu tawãlĩu mãtãda mãsu gaskiya maza da mãsu gaskiya mãtã, da mãsu haƙuri maza da mãsu haƙuri mãtã, da mãsu tsõron Allah maza da mãsu tsõron Allah mãtã, da mãsu sadaka maza da mãsu sadaka mãtã, da mãsu azumi maza da mãsu azumi mãtã da mãsu tsare farjõjinsu maza da mãsu tsare farjõjinsu mãtã, da mãsu ambaton Allah da yawa maza da mãsu ambatonsa mãtã, Allah Ya yi musu tattalin wata gãfara da wani sakamako mai girma.
( 1 ) Umurni ga mãtan Annabi umurni ne ga matãn sauran Musulmi. Sabõda haka ba ya halatta mace ta fita daga gidanta fãce da larũra.