Hausa translation of the meaning Page No 423

Quran in Hausa Language - Page no 423 423

Suratul Al-Ahzab from 36 to 43


36. Kuma ba ya halatta ga mũmini kuma haka ga mũmina, a lõkacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zãɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya sãɓã wa Allah da ManzonSa, to, yã ɓace, ɓacẽwa bayyananna. ( 1 )
37. Kuma a lõkacin ( 2 ) da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, « Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa, » kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana ( 3 ) shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin ( auren mãtan ) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa.
38. Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙã'idar, Allah a cikin ( Annabãwa ) waɗanda suka shige daga gabãninsa. Kuma umurnin Allah yã kasance abin ƙaddarãwa tabbatacce.
39. Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma sunã tsõronSa, kuma bã su tsõron kõwa fãce Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi.
40. Muhammadu bai kasance uban kõwa ba daga mazanku, kuma amma shĩ yã kasance Manzon Allah kuma cikon Annabãwa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kõme.
41. Ya ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa.
42. Kuma ku tsarkake shi, a sãfiya da maraice.
43. ( Allah ) Shĩ ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikunSa ( sunã yi muku addu'a ) , dõmin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma ( Allah ) Yã kasance Mai Jĩn ƙai ga mũminai.
( 1 ) Wannan ãyã hani ne ga kõwane Musulmi kõ Musulma ga sãɓa wa umurnin Allah da Manzonsa, su bi son rãyukansu ga kõme. Kuma ba a lõkacin auren Zainab da Zaidu ne ɗai ta sauka ba kamar yadda waɗansu mãsu tafsiri ke rubũtãwa dõmĩn an yi wannan aure a gabãnin hijira da nĩsa, ita ãyãr kuwa tã sauka a Madĩna ne a bãyan yãƙinAhzab, kamar yadda tsarin maganarta ya nũna.
( 2 ) Idan Allah ya umurci mutãne da yin wani abu kõ da barinsa to, Annabi shĩ ne mai fãra bin umurnin kõ kange kansa daga abin da aka hana. Wannan ƙissa misãli ce ga ãyarda ke a gaba da ita, yadda Annabi ya bi umurni wajen auren mãtar Zaidu bn Hãrisa wanda Annabi ya yi tabanninsaa gabãnin a hana aiwatar da tabanni. Auren yã auku Annabi na da shekara 58 ita kuwa da shekara 43. Sũnanta Zainab bintu Jahash ɗiyar goggon Annabi. Allah Yã nũna cewa dai tabanni yã mutu sõsai.
( 3 ) Abin da Annabi ke ɓoyewa shĩ ne umurnin Allah da Ya gaya masa cẽwa, zai auri Zainab mãtar Zaidu a bãyan Zaidun ya sake ta. Sabõda haka Annabi ke lallãshin Zaidu dõmin kada sakin ya auku har aurenta ya zama wãjibi akansa, a bãyan abin da aka sani na cẽwa, Zaidu yã zama ɗansa da tabanni a gabãnin haka.