Surah AlAhzab | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 426
Suratul Al-Ahzab from 55 to 62
55. Bãbu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma bãbu game da ɗiyansu, kuma bãbu game da 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma bãbu game da ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kuma bãbu game da mãtan mũminai, kuma bãbu game da abin da hannãyensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Yã kasance Mahalarci a kan kõme.
56. Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ( 1 ) ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni!Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.
57. Lalle waɗanda ke cũtar Allah da MauzonSa Allah Yã la'ane su, a cikin dũniya da Lãhira, kuma Yã yi musu tattalin azãba mai wulãkantarwa.
58. Kuma waɗanda suke cũtar mũminai maza dã muminai mãtã, bã da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne.
59. Yã kai Annabi! Ka ( 2 ) ce wa mãtan aurenka da 'yã'yanka da mãtan mũminai su kusantar da ƙasã daga manyan tufãfin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su dõmin kada a cũce su. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai Jin ƙai.
60. Lalle, idan munãfukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukãtansu, da mãsu tsẽgumi a cikin Madĩna, ba su hanu ba ( daga hãlãyensu ) , ( 3 ) lalle, zã Mu shũshũta ka a gare su, sa'an nan bã zã su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, fãce kaɗan.
61. Sunã la'anannu, inda duka aka sãme su a kãmã su, kuma a karkashe su karkashẽwa.
62. A kan hanyar Allah ( ta gyaran jama'a ) a cikin waɗanda suka shũɗe gabãninka, kuma bã zã ka sãmi musanyãwa ba ga hanyar Allah.
( 1 ) Salãtin Allah ga Annabi, shĩ ne ɗaukaka darajarsa a kõyaushe. Salãtin malã'iku, shĩne istigfãri da addu'a a gare shi. Salãtin mutãne, shĩ ne ibãda da istigfãri da addu'a a gare shi da tawassuli da shi dõmin nẽman Allah Ya karɓi ibãdarsu. Salãti sau ɗaya wãjibi ne a kan kõwane Musulmi a tsawon ransa, sa'an nankuma sunna ce a cikin kõwace salla. Kuma mustahabbi ne a cikin kõwane mazauni da wurin ambatonsa.
( 2 ) Anã fãra gyãra daga sama, sa'an nan gyãran ya sauko ƙasa, kamar ɓarnar da tã fãru daga sama, sai tã kai ƙasa.
( 3 ) Munãfukai da Shaiɗãnuda mãsu tsẽgumi bãbu abin da ke hana su mugun hãlinsu sai tasnani da tsõrõ.