Hausa translation of the meaning Page No 427

Quran in Hausa Language - Page no 427 427

Suratul Al-Ahzab from 63 to 73


63. Sunã tambayar ka ( 1 ) ga Sã'a. Ka ce: « Saninta yanã wurin Allah kawai. » Kuma me yã sanar da kai cẽwa anã tsammãnin sa'a ta kasance kusa?
64. Lalle Allah Yã la'ani kãfirai, kuma Yã yi musu tattalin wata wuta mai ƙũna.
65. Sunã madawwama a cikinta har abada, bã su sãmun majiɓinci, kuma bã su sãmun mataimaki.
66. Rãnar da ake jũya fuskõkinsu a cikin wuta sunã cẽwa, « Kaitonmu, sabõda,rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo! »
67. Kuma suka ce: « Yã Ubangijinmu! Lalle mũ mun ( 2 ) bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya! »
68. « Yã Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azãba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma. »
69. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cũci ( 3 ) Mũsã sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah.
70. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya.
71. Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gãfarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, to, lalle, yã rabbanta, babban rabo mai girma.
72. Lalle Mũ, Mun gitta amãna ga sammai da ƙasã da duwãtsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsõro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shĩ ( mutum ) ya kasance mai yawan zãlunci, mai yawan jãhilci.
73. Dõmin Allah Ya azabta munãfukai maza da munãfukai mãtã, da mushirikai maza da mushirikai mãtã, kuma Allah Yã karɓi tũba ga mũminai maza da mũminai mãtã. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara, Mai jin ƙai.
( 1 ) Shiryarwa ce ga Musulmi cẽwa idan zã su yi tambaya su tumbayi addininsu da abũbuwa mãsu amfãni a gare su, kada su tambayi abinda ya fi hankalinsukamar sa'a da abũbuwan gaibi da Allah Yã kẽɓãnta da saninsu.
( 2 ) Wannan yã nũna biya da jãhilci ga addini bã uzuri bã ne.Anã azãbtar da mai biya, kamar yadda ake azabtar da shugaban ɓata.
( 3 ) Kada ku cũci Muhammadu da ƙazafĩ kõ mũguwar magana kamar yadda Yahũdu suka yi ƙazafi ga Mũsã da nẽman wata kãruwa ta ce yã nẽme ta da zina kõ kuma da cẽwa shi mai gwaiwa ne, sai Allah Ya tsare Mũsã daga ƙazafin' kuma Ya sanya wani dũtse, ya gududa tufãfinsa daga wurin wanka har suka gan Shi mai cikakkiyar halitta ne, bãbu naƙasa game da shi. Allah Yã barrantar da shi daga dukan aibi. Haka Yake barrantar da Muhammadu ga mai son ya sa masa aibi.