Hausa translation of the meaning Page No 463

Quran in Hausa Language - Page no 463 463

Suratul Al-Zumar from 41 to 47


41. Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba.
42. Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni.
43. Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: « Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta? »
44. Ka ce: « Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku. »
45. Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasunSa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki.
46. Ka ce: « Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa. »
47. Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar Ƙiyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su.