Surah Az-Zumar | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 462
Suratul Al-Zumar from 32 to 40
32. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai?
33. Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa.
34. Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa.
35. Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa.
36. Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke waninSa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa.
37. Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa?
38. Kuma lalle idan ka tambaye su: « Wane ne ya halitta sammai da ƙasã? » Haƙĩƙa, zã su ce, « Allah ne. » Ka ce: « Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne? » Ka ce: « Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara. »
39. Ka ce: « Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani. »
40. « Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa. »