Surah Ghafir | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 469
Suratul Al-Mu'min from 17 to 25
17. Yau anã sãka wa kõwane rai a game da abin da ya aikata, bãbu zãlunci a yau. Lalle Allah Mai gaggawar hisãbi ne.
18. Kuma ka yi musu gargaɗi kan rãnar ( Sã'a ) makusanciya, a lõkacin da zukãta suke mãsu cika da bakin ciki, ga maƙõsansu. Bãbu wani masõyi ga azzãlumai, kuma bãbu wani mai cẽto da zã a yi wa dã'a ( ga cẽtonsu ) .
19. ( Allah ) Ya san yaudarar idãnu da abin da ƙirãza ke ɓõyẽwa.
20. Kuma Allah Shĩ ke yin hukunci da gaskiya, waɗannan da kuke kira, waninSa,bã su yin hukunci da kõme. Lalle Allah, Shĩ ne Mai ji, Mai gani.
21. Ashe, ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasã, dõmin su dũba ga yadda ãƙibar waɗanda suka kasance a gabãninsu ta zama? Sun kasance sũ ne mafi tsananin ƙarfi daga gare su, da kufaifan aiki a cikin ƙasã, sai Allah Ya kãmã su da laifuffukansu. Kuma bã su da wani mai tsarẽwa daga Allah.
22. Wancan sababinsa, dõmin sũ Manzanninsu sun kasance sunã zuwa gare su da hujjõji bayyanannu, sai suka kãfirta, sai Allah Ya kãmã su. Lalle Shĩ Mai ƙarfi ne, Mai tsananin azãba.
23. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã a game da ãyõyinMu da wani dalĩli bayyananne.
24. Zuwa ga Fir'auna da Hãmãna da Kãrũna, sai suka ce: « Mai sihiri ne, maƙaryaci. »
25. Sa'an nan, a lõkacin da ya jẽ musu da gaskiya daga wurinMu, suka ce: « Ku kashe ɗiyan waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi, kuma ku rãyar da mãtansu. » Kuma mugun shirin kãfirai, bai zama ba fãce a cikin bata.