Hausa translation of the meaning Page No 468

Quran in Hausa Language - Page no 468 468

Suratul Al-Mu'min from 8 to 16


8. « Ya Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su a gidãjen Aljannar zama, wannan da Ka yi musu wa'adi, sũ da wanda ya kyautatu daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu. Lalle Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima. »
9. « Kuma Ka tsare su daga mũnãnan ayyuka, kuma wanda Ka tsare shi daga mũnãnan ayyuka a rãnarnan, to, lalle, Ka yi masa rahama kuma wancan shi ne babban rabo mai girma. »
10. Lalle waɗanda suka kãfirta, anã kiran su, « Haƙĩƙa, ƙin Allah ( a gare ku ) shĩ ne mafi girma daga ƙinku ga kanku a lõkacin da ake kiran ku zuwa ga ĩmãni, sai kunã ta kãfircẽwa. »
11. Suka ce: « Ya Ubangijinmu! Kã matar da mu sau biyu, kuma Kã rãyar da mu sau biyu, sabõda haka mun yarda da laifuffukan mu. To, shin, akwai wata hanya zuwa ga fita? »
12. Wancan sababinsa, lalle ( shi ne ) idan an kirãyi Allah Shi kaɗai, sai ku kãfirta, kuma idan aka yi shirki game da Shi, sai ku yi ĩmãni. To, hukuncin fa, na Allah Maɗaukaki, Mai girma ne.
13. Shĩ ne Wanda ke nũna muku ãyõyinSa, kuma Ya saukar da arziki daga sama sabõda ku, kuma bãbu mai yin tunãni fãce mai mayar da al'amari ga Allah.
14. Sabõda haka ku kirãyi Allah, kunã mãsu tsarkake addini a gare Shi, kuma kõ dã kãfirai sun ƙi.
15. Mai ɗaukaka darajõji ( dõmin mũminai ) , Mai Al'arshi, Yanã jẽfa rũhi ( 1 ) daga al'amarinSa a kan wanda Ya so daga bãyinSa, dõmin ya yi gargaɗi kan rãnar gamuwa.
16. Rãnar da suke bayyanannu, bãbu wani abu daga gare su wanda yake iya bõyuwa ga Allah. « Mulki ga wa ya ke a yau? » Yana ga Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa.
( 1 ) Rũhi a nan, ga fahimta ta, Allah ne Mafi sani, shĩ ne karfin rai da basĩrar fahimtar addĩni da aiki wajen rãyar da shi, wanda Allah Yake sakãwa ga mãlamin da Yake nufin jaddada addini da shi a kan kõwane karni kamar yaddaHadisi ya zo da shi, ya kõre jidãlin mãsu jidãli.