Surah Ghafir | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 471
Suratul Al-Mu'min from 34 to 40
34. « Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Yusufu ya zo muku daga gabãni, da hujjõji bayyanannu, ba ku gushe ba kunã a cikin shakka daga abin da ya zo muku da shi, har a lõkacin da ya halaka kuka ce, 'Allah bã zai aiko wani Manzo ba, a bãyansa.' Kamar haka Allah ke ɓatar da wanda yake mai ɓarna, mai shakka. »
35. « Waɗanda kejayayya a cikin ãyõyin Allah, bã da wani dalĩli da ya zo musu ba. Jidalin ya girma ga zamansa abin ki a wurin Allah da wurin waɗanda suka yi ĩmãni. Kamar haka Allah ke bicẽwar haske a kan zũciyar dukan makangari, mai tĩlastãwa. »
36. Kuma Fir'auna ye ce, « Yã Hãmana! Ka gina mini bẽne, dammãnĩna zã ni isa ga ƙõfõfi. »
37. « Ƙõfõfin sammai dõmin in yi ninƙaya zuwa ga abin bautãwar Mũsã. Kuma lalle nĩ haƙĩƙa inã zaton sa maƙaryaci. » Kuma haka dai aka ƙawãce wa Fir'auna mũnãnan aikinsakuma aka danne shi daga barin tafarki. Kuma mugun nufin Fir'auna bai zama ba fãce yanã a cikin hasãra. « »
38. Kuma wannan da ya yi ĩmãni ya ce: « Ya mutãnẽna! Ku bĩ ni, in shiryar da ku tafarkin shiryuwa. »
39. « Kuma ya mutãnẽna! Wannan rãyuwa ta dũniya dan jin dãɗi ne kawai, kuma lalle Lãhira ita ce gidan tabbata. »
40. « Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a sãka masa ba fãce da misãlinsa, kuma wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji kõ mace alhãli kuwa shĩ mũmini ne, to, waɗannan sunã shiga Aljanna, anã ciyar da su a cikinta, bã da lissãfi ba. »