Hausa translation of the meaning Page No 472

Quran in Hausa Language - Page no 472 472

Suratul Al-Mu'min from 41 to 49


41. « Kuma ya mutãnẽna! Me ya sãme ni, inã kiran ku zuwa ga tsĩra, kuma kunã kira na zuwa ga wutã? »
42. « Kuna kira na zuwa ga in kãfirta da Allah, kuma in yi shirki, game da Shi, da abin da bãbu wani ilmi game da shi gare ni, kuma ni inã kiran ku zuwa ga Mabuwãyi, Mai gãfara. »
43. « Haƙƙan ne abin da kawai kuke kira na zuwa gare shi, bã ya da wani kira a cikin dũniya, kuma bã shi da shi a Lãhira kuma lalle makomarmu zuwa ga Allah take, kuma lalle mabarnata sũ ne 'yan wutã. »
44. « To zã ku ambaci abin da nake gaya muku, kuma inã fawwala al'amarina zuwa ga Allah. Lalle Allah Mai gani ne ga bãyinSa. »
45. Sai Allah Ya tsare shi daga mũnãnan abũbuwa da suka yi na mãkirci, kuma mummunar azãba ta wajaba ga mutãnen Fir'auna.
46. Wutã, anã gitta su a kanta, sãfe da maraice, kuma a rãnar da Sa'a take tsayuwa, anã cẽwa, « Ku shigar da mutãnen Fir'auna a mafi tsananin azãba. »
47. Kuma a lõkacin da suke husũma a cikin wutã, sai raunãna ( mabiya ) su ce wa waɗanda suka kangara ( shugabanni ) , « Lalle mũ, mun kasance mabiya gare ku, to, shin kũ mãsu wadãtar da mu ne daga barin wani rabo daga wutã? »
48. Waɗanda suka kangara suka ce: « Lalle mũ duka munã a cikinta. Lalle ne, Allah Ya yi hukunci a tsakãnin bãyinSa. »
49. Kuma waɗanda suke a cikin wutã suka ce wa matsaran Jahannama, « Ku rõki Ubangijinku Ya sauƙaƙa mana ,a yini ɗaya, daga azãba. »