Hausa translation of the meaning Page No 486

Quran in Hausa Language - Page no 486 486

Suratul Al-Shura from 23 to 31


23. Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyinSa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: « Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta. » Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya.
24. Kõ zã su ce: « Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne? » To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata.
25. Kuma Shi ne ke karɓar tũba daga bãyinSa, kuma Yanã Yafe ƙananan laifuffuka, alhãli kuwa Yanã sanin abin da kuke aikatãwa.
26. Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu ( sakamako ) daga falalarSa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani.
27. Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani.
28. Kuma Shĩ ne ke sassaukar da girgije ( ruwa ) a bãyan sun yanke ƙauna kuma Yana wãtsa rahamarSa, alhãli kuwa Shĩ ne Majiɓinci, Mai gõdiya.
29. Kuma akwai daga ãyõyinSa, halittar sammai da ƙasa da abin da Ya wãtsa a cikinsu na dabba alhãli kuwa Shĩ Mai ĩko ne ga tãra su, a lõkacin da Yake so.
30. Kuma abin da ya sãme ku na wata masifa, to, game da abin da hannãyenku suka sana' anta ne kuma ( Alah ) Yanã Yafẽwar ( waɗansu laifuffuka ) mãsu yawa.
31. Kuma ba ku zama mãsu buwãya ba a cikin ƙasa kuma bã ku da wani majiɓinci, wanin Allah, kuma bã ku da wani mataimaki.