Surah Ash-Shura | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 487
Suratul Al-Shura from 32 to 44
32. Kuma akwai daga ãyõyinsa, jirãge mãsu gudãna a cikin tẽku kamar duwãtsu.
33. Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun,Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya.
34. Kõ Ya halakã su ( sũ jirãgen ) sabõda abin da mãsu su suka sanã'anta, alhãli kuwa Yanã yãfe ( laifuffuka ) mãsu yawa.
35. Kuma dõmin waɗanda ke jãyayya a cikin ãyõyinMu su sani ( cẽwa ) bã su da wata mafaka.
36. Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci,kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai.
37. Kuma waɗanda ( 1 ) ke nisantar manyan zunubbai da ayyukan alfãsha, kuma idan sun yi fushi, sũ, sunã gãfartawa.
38. Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa.
39. Da waɗanda ( 2 ) idan zãlunci ya sãme su, sunã nẽman taimako ( su rãma ) .
40. Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ ( Allah ) bã Ya son azzãlumai.
41. Kuma Lalle ne, wanda ya nẽmi taimakon rãmãwa a bãyan an zãlunce shi, to waɗannan bãbu wata hanyar zargi a kansu.
42. lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi.
43. Kuma Lalle ne, wanda ya yi haƙuri kuma ya gãfarta ( wa wanda ya zãlunce shi ) , to shĩ wancan aiki haƙĩƙa, yanã daga manyan al'amura ( da Allah ke so ) .
44. Kuma wanda ( 3 ) ( Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyanSa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, « Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa? »
( 1 ) Bayãnin siffõfin mũminai, waɗanda suke tsare su, Yana lãmunce zama haɗe, da gamuwar Musulmi, sũ ne siffõfi shida, nisantar manyan zunubbai da zina, da gãfarta fushi, da tsayar da salla, da shãwara ga al'amuran tsakãninsu, da ciyar da dũkiya da ta wajabci mutum ya ciyar da ia a cikin alhẽri ga inda Allah Ya ce a ciyar da ita.
( 2 ) Wajen rãma zãlunci kõ yinsa, mutãne sun kasu kashi huɗu. Mãsu rãmãwa gwargwadon zãlunci, bã su da laifi; da mãsu rãmãwa da abin da ya fi laifin da aka yi musu, to, sunã da laifi kamarmãsu fãra zãlunci, da mãsu gãfartãwa, waɗannan sũ ne Allah ke so.
( 3 ) Bayãnin mai zãlunci da sakamakonsa a Rãnar Lãhira.