Hausa translation of the meaning Page No 512

Quran in Hausa Language - Page no 512 512

Suratul Al-Fath from 10 to 15


10. Lalle waɗanda ke yi maka mubãya'a, ( 1 ) Allah kawai ne suke yi wa mubãya'a, Hannun Allah nã bisa hannayensu, sabõda haka wanda ya warware, to, yanã warwarẽwa ne a kan kansa kawai, kuma wanda ya cika ga alkawarin da ya yi wa Allah a kansa, to, ( Allah ) zai kãwo masa ijãra mai girma.
11. Waɗanda aka bari daga ƙauyãwa ( 2 ) zã su ce maka, « Dũkiyõyinmu da iyãlanmu sun shagaltar da mu, sai ka nẽma mana gãfara. » Sunã faɗã, da harsunansu, abin da bã shĩ ne a cikin zukãtansu ba. Kace: « To, wãne ne ke mallakar wani abu daga Allah sabõda kũ, idan Yã yi nufin wata cũta agare ku kõ kuma ( idan ) Ya yi nufin wani amfãni a gare ku? Ã'a, Allah Ya kasance Mai labartawa ne ga abin da kuke aikatãwa. »
12. Ã'a kun yi zaton Annabi da mũminai, bã za su kõmo zuwa ga iyãlansu ba, har abada. Kuma an ƙawãta wannan ( tunãni ) a cikin zukãtanku, kuma kun yi zato, zaton mugunta, kuma kun kasance mutãne halakakku.
13. Kuma wanda bai yi ĩmãni da Allah da kuma Manzonsa ba, to, lalle Mũ, Mun yi tattalin wutã mai tsananin ƙũna, dõmin kafirai.
14. Mulkin sammai da ƙasã na Allah kawai ne, Yanã gãfartawa ga wanda Yake so, kuma Yanã azabta wanda Yake so alhãli kuwa Allah Ya kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
15. Waɗanda aka bari zã su ce idan kun tafi zuwa ga waɗansu ganĩmõmi ( 3 ) dõmin ku karɓo su, « Ku bar mu, mu bĩ ku. » Sunã son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: « Bã zã ku bĩ mu ba. Kamar wannan ne Allah Ya ce, a gabãnin haka. » Sa'an nan zã su ce: « Ã'a, kunã dai hãssadar mu ne. » Ã'a, sun kasance bã su fahimtar ( abũbuwa ) sai kaɗan.
( 1 ) Asalin mubãya'a daga bai'u ne, watau ciniki, wanda ya yi mubãya'a ga Limãmin Musulmi kamar yã yi ciniki, ne yã sayar da ransa, dõmin ya karɓi Aljanna daga Allah a Rãnar Ƙiyãma. Mubãya'a ta farko,ita ce wadda aka yi wa Annabi a Hudaibiyya wani ɗan gari ne kusa da Makka a hanyar Jadda, tafiyar kwana ɗaya. An ce tanã a cikin Hurumi, waɗansu sun ce bã ta cikinsa.
( 2 ) Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya yi nufin tafiya Makka dõmin ya yi Umra sabõda mafarkin da ya yicẽwa yã ga ya shiga Makka shi da Sahabbansa, sunã mãsu yin aski da suisuye na ibãda, sai ya ce wa ƙauyãwan da ke gẽfen Madina su fita tãre da shi dõmin kada Ƙuraishãwa su fãɗa shi da yãƙi,su tsare shi daga Ɗãkin. Kuma ya yi harama ya kõra hadaya dõmin mutãne su san bã yãƙi yake nufi ba. Sai waɗansu mãsu yawa daga ƙauyãwa suka yi nauyin fita, sukayi zamansu kuma suka ce: « Zai tafi zuwa ga mutãnen da suka yãƙe shi a tsakar gidansa a Madĩna, suka kashe Sahabbansa. Ba zã mu bĩ shi ba dõmin mu halakakanmu. »
( 3 ) A bãyan sulhun Hudaibiyya Allah Ya yi wa Annabi alkawarin zai buɗe masa Haibara ya sãmi ganĩma mai yawa, amma kuma kada ya bari ƙauyãwan da aka nema su fita zuwa Makka, suka ƙi su fita tãre da shi.