Surah Al-Fath | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 513
Suratul Al-Fath from 16 to 23
16. Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: « Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne ( 1 ) mãsu tsananin yãƙi ( dõmin ) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi. »
17. Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, ( Allah ) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, ( Allah ) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.
18. Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a ( 2 ) a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.
19. Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima.
20. Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta ( 3 ) muku wannan. Kuma Ya kange ( 4 ) hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.
21. Da waɗansu ( ganĩmõmin ) ( 5 ) da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme.
22. Kuma dã waɗanda suka kãfirta sun yãke ku, dã sun jũyar da ɗuwaiwai ( dõmin gudu ) sa'an nan bã zã su sãmi majiɓinci ba, kuma bã zã su sãmi mataimaki ba.
23. Hanyar Allah wadda ta shũɗe daga gabãnin wannan, kuma bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah ( ta taimakon mũminai akan mai zãluntarsu ) .
( 1 ) Abũbakar zai kira su dõmin su yãƙi mutãnen Musailama, ko kuma su yãƙi Rũmu da fãrisa a bãyan rãyuwar Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi.
( 2 ) A bãyan da Annabi ya saukaa Hudaibiyya, ya kirãyi Khuraish bn Umaiya el Khuzã'i ya aike shi Makka ya azã shi a kan rãƙuminsa dõmin ya gaya wa shugabanninsu cẽwa yãtaho Umra ne, bai zo da yãƙi ba. Sai suka sõke rãƙuminAnnabi, kuma suka yi nufin kashe Khuraish amma Ahãbish suka hana su, ya zo ya gaya wa Annabi. Sa'an nan Annabi ya kira Umar bn Khattãb dõmin ya aika shi zuwa Makka, ai ya ce: « Ya Manzon Allah inã tsõron raina ga Ƙuraishãwa, bãbu banĩ Adiyyin bnKa'ab a Makka balle su kare ni daga gare su, amma inã nũna maka wani mutum wanda ya fĩ ni dangi a cikinta shĩ ne Usman bn Affãn. » Sai Annabi ya kira Usman ya aike shi zuwa ga Abi sufyãn da shugabannin Ƙuraish, ya bã su lãbãrin cẽwa bai zo yãƙi ba. ya taho ne dõmin ziyãra kawai ga wannan Ɗãki dõmin ya girmama alfarmarsa. Ya rubũta masa takarda ya tafi da ita. Kuma ya umurce shi da ya yi bushãra ga Musulmi mãsu rauni, cẽwa cin nasara yã yi kusa, kuma Allah zai ɗaukaka addininsa. Usman ya fita ya tafi Makka ya iske cẽwa Ƙuraishãwa sun haɗu a kaĩn hana Annabi shiga Makka. Abban bn sa'ĩd bn Asi ya haɗu da Usman a lõklcin shigarsa Makka, sai ya ɗauke shi a kan rãƙumarsa, ya bã shi maƙwabtaka dõmin kada a kashe shi, har ya kai takardar Annabi. Suka nãce cẽwa Annabi bã zai shiga ba suka ce wa Usmãn: « Idan yanã son ɗawãfi sai ya yi, » Sai ya ce bã zai yi ba sai Manzon Allah ya yi. Musulmi suka ce: « Usmãn ya ji daɗi yã yi ɗawafi, » sai Annabi ya ce: « Ban yi zatonUsmãn zai yi ba. » Sa'an nan lãbãri ya zo wa Annabi, cẽwa an kashe Usmãn sabõda haka Annabi ya ce: « Idan sun kashe shi, sai mun yaƙe su. » Wannan ya sa aka yi masa mubãya'a a ƙarƙashin itãciyar ɗalh mai kama da farar ƙaya. A bãyan haka Annabi ya aza hannunSa na hagu a kan hannunsa na dãma, ya ce: « Gã hannun Usmãnu. » Mãsu mubãya'a dubũ da ɗari uku kõ ɗari huɗu ne, da cẽwa za su yi yãƙi da Ƙuraishawa, bã zãsu gudu ba, sai dai su mutu. Daga nan shugabancin ya tabbata. Umar bn Khattãb yã sanya an sãre itãciyar nan dõmin mutãne sun fãra salla a ƙarƙashinta. Ba a yi yãƙi ba, sai aka yi sulhu. Annabi ya kõma a shẽkara mai zuwa yã yi Umra.
( 3 ) Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshenzul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shẽkara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta.
( 4 ) A lõkacin da Annabi ya fitadaga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su jẽ su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jẽfa tsõro a cikin zukãtansu.
( 5 ) Ganĩma da aka yi musu gaggãwa da ita, ita ce Hlibara. Ganĩma wadda ba su da ĩko da ita, ita ce sauran ƙasãshen dũniya inda Musulmi suka ci, suka mallake shi, na ƙasar Rumãwa da farisãwa da Masar da sauransu.