Hausa translation of the meaning Page No 53

Quran in Hausa Language - Page no 53 53

Suratul Al-Imran from 23 to 29


23. Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littãfi ba ana kiran su zuwa ga Littãfin Allah dõmin ya yi hukunci a tsakãninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta jũya bãya, kuma sunã mãsu bijirẽwa?
24. Wannan kuwa, dõmin lalle ne su sun ce: « Wutã bã zã ta shãfe mu ba, fãce a 'yan kwãnaki ƙidãyayyu. » Kuma abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa na ƙarya ya rũɗẽ su a cikin addininsu.
25. To, yãya idan Mun tãra su a yini wanda bãbu shakka a cikinsa, kuma aka cikã wa kõwane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhãli kuwa, sũ bã zã a zãlunce su ba?
26. Ka ce: ( 1 ) « Yã Allah Mamallakin mulki, Kanã bayar da mulki ga wanda Kake so, Kanã zãre mulki daga wanda Kake so, kuma Kanã buwãyar da wanda Kake so, kuma Kanã ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alhẽri yake. Lalle ne Kai, a kan kõwane abu, Mai ĩkon yi ne. » « Kanã shigar da dare a cikin yini, kuma Kanã shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kanã fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kanã azurta wanda Kake so bã da lissafi ba. »
28. Kada mũminai su riƙi kãfirai masõya, baicin mũminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kõme ba daga Allah, fãce fa dõmin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kãriya. Kuma Allah yana tsõratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makõma take.
29. Ka ce: « Idan kun ɓõye abin da ke a cikin ƙirãzanku, kõ kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kõwane abu Mai ĩkon yi ne. »
( 1 ) Wato ka mayar da ĩkon kõme ga Allah, yana yin sa yandaYake so, bãbu mai iya hanãwa, sa'an nan kuma ka ce wamũminai, kada su yi wata mu'amala da kãfirai, su bar yan'uwansu mũminai, sai dai a kan lalũra kawai. Wanda ya riƙi kãfirai ya bar mũminai, to, bã shi tãre da Allah a cikin kõme.
27.