Surah Al-Imran | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 54
Suratul Al-Imran from 30 to 37
30. A Rãnar da kõwane rai yake sãmun abin da ya aikata daga alhẽri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhãli yana gũrin, dã dai lalle a ce akwai fage mai nĩsa a tsakãninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yanã tsõratar da kũ kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bãyinSa.
31. Ka ce: « Idan kun kasance kunã son Allah to, ku bĩ ni, Allah Ya sõ ku, kuma Ya gãfarta muku zunubanku. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai. »
32. Ka ce: « Ku yi ɗã'a ga Allah da Manzo. » To, amma idan sun jũya bãya, to, lalle ne Allah bã Ya son kãfirai.
33. Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai.
34. Zuriyya ce sãshensu ( 1 ) daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
35. A lõkacin da mãtar Imrãna ( 2 ) ta ce: « Ya Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani. »
36. To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: « Ya Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace! » KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa. « Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu ( 3 ) kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe. »
37. Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. ( Sai kuwa ) ya ce: « Yã Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki? » ( Sai ) ta ce: « Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba. »
( 1 ) Sũ duka daidai suke ga mai da al'amari ga Allah.
( 2 ) Mãtar Imrãna sunanta Hannatu ɗiyar fãƙũza, bã ta haifuwa, sai wata rãna ta ga tsuntsuwa tanã ciyar da tsãkonta,sai ta yi sha'awar sãmun ɗa sabõda haka ta rõki Allah Ya bã ta ɗa. Da mijinta Imrãna ya tãke ta sai ta sãmi ciki, dõmin murna sai ta yi alkwarin 'yanta shi da bakance ga Masallacin Baitil Muƙaddas dõmin ya riƙa yi masahidima. To, a lõkacin da ta haihu sai ta sãmi ɗiya mace. Ga shari'arsu bã a 'yanta mace ga irin wannan aiki na hidimar masallaci, dõmin haka ta nẽmi uzuri da cẽwa ta haife ta mace, mace bã kamar namiji take ba. Har ta yi ruɗu ta jũya, ta ce, namijin, bã kamar mace ba, dõmin namiji ne a cikin zũciyarta.
( 3 ) Maryam, ma'anarta mai ibãda. Abinci da ake kai mata a cikin Masallaci shĩ ne 'ya'yan itãce, irin na ɗãri, a lõkacin bazara, kuma irin na bazara a lõkacin ɗãri. Wannan kuma ya mõtsar da bẽgen zakariyya ga sãmun ɗã, bãyan shi da mãtarsa sun tsũfa ba su haifu ba. Sai ya rõƙi Allah kuma Ya karɓa masa, Ya ba shi Yahaya Annabi.