Hausa translation of the meaning Page No 581

Quran in Hausa Language - Page no 581 581

Suratul Al-Mursalat from 20 to 50


20. Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba.
21. Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce.
22. Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna.
23. Sa'an nan, Muka nũna iyãwarMu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa.
24. Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
25. Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba.
26. Ga rãyayyu da matattu,
27. Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi?
28. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
29. Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi!
30. Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku.
31. Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta.
32. Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye.
33. Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe.
34. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
35. Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba.
36. Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari.
37. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
38. Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko.
39. To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita.
40. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
41. Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari.
42. Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari.
43. ( A ce musu ) « Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa. »
44. Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
45. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
46. ( Ana ce musu ) « Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne. »
47. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
48. Kuma, idan an ce musu: « Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in ( salla ) ba. »
49. Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
50. To, da wane lãbãri ( Littãfi ) , waninsa ( Alƙur'ãni ) zã su yi ĩmãni