Hausa translation of the meaning Page No 580

Quran in Hausa Language - Page no 2 2

Suratul Al-Dahr from 26 to 19


26. Daga dare, sai ka yi sujũda gare Shi, kuma ka tsarkake Shi darẽ mai tsawo.
27. Lalle ne, waɗannan suna son mai gaugãwa ( dũniya) kuma suna bari, a bãyansu, wani yini mai nauyi.
28. Mũ ne Muka halitta su kuma Muka, ƙarfafa halittarsu, kuma idan Mun so, za Mu musanyâ su da wasu mutane kwatankwacinsu, musanyawa.
29. Lalle ne, wannan wata tunãtarwa ce, saboda wanda ya so ya riƙa hanyar kirki zuwa ga Ubangijinsa.
30. Kuma, bã zã ku so ba, sai Allah Ya so, lalle ne Allah Yã kasance Masani' Mai hikima.
31. Yana shigar da wanda Ya so a cikin rahamarsa, kuma azzãlumai, Yã yi musu tattalin wata azãba mai raɗaɗi.
Sũratul Mursalãt
Tana gargaɗi dõmin nẽman a gaskata Alƙur’ãni da abin da yake faɗa game da Ƙiyãma.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna.
2. Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi.
3. Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa.
4. sa'an nan, da ãyõyi ( 1 ) mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa.
5. Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni.
6. Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi.
7. Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
8. To, idan taurãri aka shãfe haskensu.
9. Kuma, idan sama aka tsãge ta.
10. Kuma, idan duwãtsu aka nike su.
11. Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su.
12. Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali.
13. Domin rãnar rarrabẽwa ( 2 ) .
14. Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa?
15. Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa!
16. Ashe, ba Mu halakar da ( mãsu ƙaryatãw ) na farko ba.
17. Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe?
18. Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi.
19. Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa!
( 1 ) Yã kamanta Manzanin Allah masu kãwo ayõyinsa da iskõki mãsu kãwo ruwa dõmin rahamar da ke cikin kowannensu.
( 2 ) Yin hukunci a tsakanin tãlikai.