Hausa translation of the meaning Page No 584

Quran in Hausa Language - Page no 584 584

Suratul Al-Nazi'at from 16 to 46


16. A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã?
17. Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi.
18. « Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka. »
19. « Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoronSa? »
20. Sai ya nũna masa ãyar ( 1 ) nan mafi girma.
21. Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa ( umurni ) ,
22. Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri.
23. Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira.
24. Sai ya ce: « Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka. »
25. Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko.
26. Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah.
27. Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta.
28. Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta.
29. Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta.
30. Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta.
31. Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta.
32. Da duwatsu, Yã kafe ta.
33. Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku.
34. To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo.
35. Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata.
36. Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani.
37. To, amma wanda ya yi girman kai.
38. Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, ( wato dũniya ) .
39. To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma.
40. Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai.
41. To, lalle ne Aljanna ita ce makõma.
42. Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta?
43. Me ya haɗã ka da ambatonta?
44. Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake.
45. Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta.
46. Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa.
( 1 ) Ãyar Mũsã da ta fi girma ita ce sandarsa mai zama maciji ko hannunsa mai haske kamar tõcila idan yã sanya cikin hammata yã fitar.