Hausa translation of the meaning Page No 583

Quran in Hausa Language - Page no 583 583

Suratul Al-Naba from 31 to 15


31. Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo.
32. Lambuna da inabõbi.
33. Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna.
34. Da hinjãlan giya cikakku.
35. Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa.
36. Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa.
37. Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi.
38. Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai.
39. Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa.
40. Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: « Kaitona, dã dai nã zama turɓãya! »
Sũratun Nãzi’ãt
Tanã karantar da cewa jinkirin saukar azãba ga mai laifi bã ƙyãle shi ba ne, ga Allah, istidrãji ne.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka ( na kafirai ) da ƙarfi.
2. Da mãsu ɗibar rãyuka ( na mũminai ) da sauƙi a cikin nishãɗi.
3. Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo.
4. Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa ( da umurnin Allah ) kamar suna tsẽre.
5. Sa,an nan, su kasance masu shirya gudanar da umurni.
6. Rãnar da mai girgiza abũbuwa ( bũsar farko ) zã ta kaɗa.
7. Mai biyar ta ( bũsa ta biyu ) nã biye.
8. Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne.
9. Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu.
10. Sunã cẽwa « Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu? »
11. « Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu? »
12. Suka ce: « Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya! »
13. To, ita kam, tsãwa guda kawai ce.
14. Sai kawai gã su a bãyan ƙasa.
15. Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka?