Hausa translation of the meaning Page No 60

Quran in Hausa Language - Page no 60 60

Suratul Al-Imran from 78 to 83


78. Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littãfi dõmin ku yi zaton sa daga Littãfin, alhãli kuwa bã shi daga Littãfin. Kuma suna cẽwa: « Shi daga wurinAllah yake. » Alhãli kuwa shi, bã daga wurin Allah yake ba. Sunã faɗar ƙarya ga Allah, alhãli kuwa sunã sane.
79. Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutãne: « Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah. » Amma ( zai ce ) : « Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa ( 1 ) . »
80. Kuma ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan kun riga kun zama mãsu sallamãwa ( Musulmi ) ?
81. Kuma a lõkacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabãwa: « Lalle ne ban bã ku wani abu ba daga Littãfi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatãwa ga abin da yake tãre da ku; lalle ne zã ku gaskata Shi, kuma lalle ne zã ku taimake shi. » Ya ce: « Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawarĩNa a kan wannan a gare ku? » suka ce: « Mun tabbatar. » Ya ce: « To, ku yi shaida, kuma Nĩ a tãre da ku Inã daga mãsu shaida. »
82. To, waɗanda kuma suka jũya bãya a bãyan wannan, to, waɗannan sũ ne fãsiƙai.
83. Shin wanin Addinin Allah suke nẽma, alhãli kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan sõ da ƙĩ, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su?
( 1 ) Wannan ya nũna karatun Alƙur'ãni kawai bã da sanin ma'anarsa ba, dõmin a yi aiki da shi, ba ya isar mutum. Amman wanda ya kõyi ibãda sõsai, sa'an nan ya karanta Alƙur'ãni, to, zã a bã shi lãda kõ dã ba ya fahimtar ma'anarsa.