Hausa translation of the meaning Page No 65

Quran in Hausa Language - Page no 65 65

Suratul Al-Imran from 116 to 121


116. Lalle ne waɗanda suka kãfirta, dũkiyõyinsu kõ ɗiyansu bã zã su wadatar musu da kõme ba daga Allah kuma waɗannan abõkan wuta ne, sũ, acikinta, madawwama ne.
117. Misãlin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rãyuwar dũniya, kamar misãlin iska ce ( wadda ) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sãmi shukar wasu mutãne waɗanda suka zãlunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zãlunce su ba, amma kansu suka kasance sunã zãlunta.
118. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku riƙi abõkan asĩri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gũrin abin da zã ku cũtu da shi. Haƙĩka, ƙiyayya tã bayyana daga bãkunansu, kuma abin da zukãtansu ke ɓõyẽwane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ãyõyi, idan kun kasance kunã hankalta.
119. Gã ku yã waɗannan! Kunã son su bã su son ku, kuma kuna ĩmãni da Littãfi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce « Mun yi ĩmani » . Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yãtsu a kanku don takaici. Ka ce « Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza. »
120. Idan wani alhẽri ya shãfe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cũtar ta shãfe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu bã ya cũtar ku da kõme. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatãwa Mai kẽwayẽwa ne.
121. Kuma a lõkacin ( 1 ) da ka yi sauko daga iyãlanka kana zaunar da mũminai a wurãren zamadõmin yãƙi, kuma Allah Mai ji ne, Masani.
( 1 ) Misãli ne ga cẽwa idan kun yi ĩmãni, kuma kun yi taƙawa, to, ƙullinsu bã ya cũtar da ku da kõme, dõmin abin da ya auku a Yãƙin Uhdu ya isa misãli ga cẽwa, sai kun karkace daga hanya sa'an nan waniabu zai sãme ku. Asalin maganar shĩ ne, Annabi yã fita Uhdu da mutum ɗari tarada hamsin kuma kãfirai sunã dubũ uku. Annabi ya sauka a Uhdu rãnar Asabat, bakwai ga Shawwal, shekara ta uku ga Hijira, ya sanya bayansa wajen dũtsen Uhdu, ya gyãra safũfuwan mayãƙa, kuma ya zaunar da wata runduna ta maharba a gefẽn dũtsen da shugabancin Abdullahi ɗan Jubair. Sa'an nan ya ce musu: « Ku kãre mu da harbi, kada su zo mana daga bãya, kada ku ɗaga daga nan, mun rinjãya kõ an rinjãye mu. » Saisuka sãɓã wa umurnin, don haka masĩfar Uhdu ta auku.