Surah Al-Imran | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 66
Suratul Al-Imran from 122 to 132
122. A lõkacin da ƙungiyõyi ( 1 ) biyu daga gare ku suka yi niyyar su karye, kuma Allah ne Majiɓincinsu, don haka, ga Allah mũminai sai su dogara.
123. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Allah Yã taimake ku a Badar, alhãli kuwa kunã mafiya rauni, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa tsammãninku, kuna gõdẽwa.
124. A lõkacin da kake cẽwa ga mũminai, « Shin bai ishe ku ba, Ubangijinku Ya taimake ku da dubu uku daga malã'iku saukakku? »
125. « Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙãre ku da dubu biyar daga malãiku mãsu alãma. »
126. Kuma Allah bai sanya shi ( 2 ) ba, fãce dõmin bushãra a gare ku, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba fãce daga wurin Allah, Mabuwãyi, Mai hikima.
127. Dõmin Ya katse wani gẽfe daga waɗanda suka kãfirta ko kuma Ya ƙasƙantã su, har su jũya, suna mãsu ruɓushi.
128. Bãbu kõme a gare ka game da al'amarin ( shiryar da su banda iyar da manzanci ) . Ko Allah Ya karɓi tũbarsu, kõ kuwa Ya yimusu azãba, to lalle ne sũ, mãsu zãlunci ne.
129. Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gãfarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
130. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku ci riba ninkininki, riɓanye, kuma ku bi Allah da taƙawa, tsammãninku zã ku ci nasara.
131. Kuma ku ji tsõron wutã wadda aka yi tattali dõmin kãfirai.
132. Kuma ku yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, tsammaninku a yi muku rahama.
( 1 ) Banũ salimah da Banũ Hãrisa sun tãshi kõmãwa gida su bar yãƙi, a lõkacin da Ubayyi bn salũl ya kõma da jama'arsa, Allah Ya tsare musu ĩmãninsu, ba su kõma ba. Watau yana cẽwa idan wani abu na masĩfa ya sãme ku, to, kun sãɓã wa Allah ne kamar yadda ya auku a Uhdu, suka sanya Annabi ya fito daga Madĩna kuma maharba suka bar wurinda aka ayyana musu. Amma kuma ai Allah Ya Taimake ku, a Badar a lõkacin da ƙarfinku bai kai haka ba, sabõda rashin saɓawarku ga umurninSa.
( 2 ) Taimako da mala'iku.