Surah An-Nisa | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 95
Suratul Al-Nisa from 102 to 105
102. Kuma idan kã kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tãre da kai, kuma sai su riƙe makãmansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bãyanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam ( ta ) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tãre da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makãmansu. Waɗanda suka kãfirta sun yi gũrin dã dai kuna shagala daga makamanku da kãyanku dõmin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma bãbu laifi, a kanku idan wata cũta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, kõ kuwa kun kasance mãsu jinya ga ku ajiye makãmanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Yã yi tattali, ga kãfirai, azãba mai walakantarwa.
103. Sa'an nan idan kun ƙãre salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sãsanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla tã kasance a kan mũminai, farilla mai ƙayyadaddun lõkuta.
104. Kuma kada ku sassauta a cikin nẽman mutãnen idankun kasance kuna jin zõgi, to, lalle sũ ma, suna jin zõgi kamar yadda kuke jin zõgi. Kuma kuna tsammãni, daga Allah, abin da bã su tsammãni. Kuma Allah Yã kasance Masani Mai hikima.
105. Lalle ne, Mũ, Mun saukar ( 1 ) , zuwa gare ka, Littãfi da gaskiya, dõmin ka yi hukunci a tsakãnin mutãne da abin da Allah Ya nũna maka, kuma kada ka kasance mai husũma dõmin mãsu yaudara.
( 1 ) Gudãnar da hukunci a cikinmahakama, kada mai shari'a ya taimaki kowane sãshe, duk yadda suke a gare shi, sai ya ɗauke su daidai a gabansa, kamar yadda ya auku a gaban Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi. Wani mutum Musulmi ana ce masa Mat'ama bn Ubairak ya yi sãtar sulke ya ɓõye shi a wurin wani Bayahũde. A lõkacin da aka gãne sulken a wurin Bayahũden, sai Mat'ama ya yi masa ƙazafi da sãtarsa, shi kuma yayi rantsuwa cewa bã shi ne ya sãtã ba. Kuma mutãnensa suka rõƙi Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gare shi, dõmin ya yi musu jãyayya yakuɓutar da mat'ama, Annabi kuwa bai yarda ba. Kamar yadda ãyõyin nan suka bayyana, domin ya zama abin kõyi. Wannan kuma ya nũna cewa,ga gudãnar da sharĩ'a Annabi yana yin ijtihãdi gwargwadon abin da ya bayyana daga hujjoji ya yi hukunci, kamar wajen shãwara a wurin yãki. Ya zama abin kõyi.