Hausa translation of the meaning Page No 94

Quran in Hausa Language - Page no 94 94

Suratul Al-Nisa from 95 to 101


95. Mãsu zama ( 1 ) daga barin yãƙi daga mũminai, wasun ma'abũta larũra da mãsu jihãdi a cikin hanyar Allah da dũkiyõyinsu da rãyukansu, bã su zama daidai. Allah Yã fĩfĩta mãsu jihãdi da dũkiyoyinsu da rãyukansu a kan mãsu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Yã yi musu alkawari da abu mai kyau ( 2 ) . Kuma Allah yã fĩfĩta mãsu jihãdi a kan mãsu zama da lãda mai girma.
96. Darajõji daga gare Shi da gãfara da rahama. Kuma Allah Yã kasance Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
97. Lalle ne, waɗanda malã'ĩku ( 3 ) suka karɓi rãyukansu, ( alhãli ) sunã mãsu zãluntar kansu,sun ce ( musu ) : « A cikin me kuka kasance? » ( Su kuma ) suka ce: « Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa. » Suka ce: « Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, dõmin ku yi hijira a cikinta? » To, waɗannan makõmarsu Jahannama ce. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
98. Fãce waɗanda aka raunana daga maza da mãtã da yãra waɗanda bã su iya yin wata dabãra, kuma bã su shiryuwa ga hanya.
99. To, waɗannan akwai tsammãnin Allah Ya yãfe laifi daga gare su, kuma Allah Yã kasance Mai yãfẽwa ne, Mai gãfara.
100. Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar ( 4 ) Allah, zai sãmu, a cikin ƙasa, wurãren jũyãwa mãsu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, lãdarsa tã auku ga Allah, Kuma Allah Yã kasance, a gare ku, Mai gãfara, Mai jin ƙai.
101. Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, bãbu laifi a kanku ku rage ( 5 ) daga salla idan kun ji tsõron waɗanda suka kãfirta su fitine ku. Lalle ne kãfirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne.
( 1 ) Falalar mãsu jihãdi a kan waɗanda ba su jihãdi daga cikin muminai. Faɗar falalar tana ƙarfafa zukãta ga yin jihãdi domin tsaron addinida rãyukan mãsu rauni da dũkiyarsu.
( 2 ) Aljanna.
( 3 ) Hukuncin rashin hijira zuwawurin yardar Allah dõmin tsayar da haƙƙõƙin Allah. Hukuncin mai dogewa ne, idan an sãmi dalĩlin yin hijirar, kuma bãbu abin da ya hana ta na uzurori.
( 4 ) Allah Yana kwaɗaitar da mũminai ga yin hijira zuwa wurin neman yardarsa. Hukuncin hijira yana nan a ko da yaushe hãli ya hukunta da a yi ta.
( 5 ) Rage salla a nan ba ana nufin sallar kasaru ta tafiya ba, wanda take ta tabbata da sunna. Wannan rage salla, shi ne sallar tsõro wadda ake yi gwargwadon hãlin da ake ciki na tsõro. Idan yana yiwuwa a yi ta da lĩmãmi, sai ya kasa jama'a kashi biyu, to, sai a yi kamar yadda ãya ta tafe zã ta yi bayãni, idan kuwa bã zai yiwu ba, sai a yi yadda hãli ya sauƙaƙa duka, kamar a ãyã ta 239 daga Suratul Baƙara.