Surah An-Nisa | from the moshaf in arabic uthmani
Listen mp3 | Tafsir Arabic | tafsir mokhtasar |
English | Indonesian | French |
German | Hausa | Spanish |
Hausa translation of the meaning Page No 97
Suratul Al-Nisa from 114 to 121
114. Bãbu wani alhẽri a cikin mãsu yawa daga gãnawarsu ( 1 ) fãce wanda ya yi umurni da wata sadaka kõ kuwa wani alhẽri kõ kuwa gyãra a tsakãnin mutãne. Wanda ya aikata haka dõmin nẽman yardõdin Allah to zã Mu bã shi lãda mai girma.
115. Kuma wanda ya sãɓã wa ( 2 ) Manzo daga bãyan shiriya tã bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar mũminai, zã Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙõne shi da Jahannama. Kuma tã mũnana ta zama makõma.
116. Lalle ne, Allah ba Ya gãfarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gãfarta abin da yake bãyan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nĩsa. ( 3 )
117. Bã su kiran kõwa, baicin Shi, fãce mãtã kuma bã su kiran kõwa fãce Shaiɗan, mai tsaurin kai.
118. Allah Yã la'ane shi. Kuma ya ce: « Lalle ne, zã ni riƙi rabõ yankakke ( 4 ) , daga bãyinKa. »
119. « Kuma lalle ne, inã ɓatar da su, kuma lalle ne inã sanya musu gũri, kuma lalle ne ina umurnin su dõmin su kãtse ( 5 ) kunnuwan dabbõbi, kuma lalle ne inã umurnin su dõmin su canza halittar Allah. » Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙĩƙa yã yi hasara, hasara bayyananniya.
120. Yanã yi musu alkawari, kuma yanã sanya musu gũri, alhãli Shaiɗan bã ya yi musu wani wa'adĩn kõme face ruɗi.
121. Waɗannan matattararsu Jahannama ce, kuma bã sãmun makarkata daga gare ta.
( 1 ) Hukuncin gãnawa da Annabiko wani shũgaban jama'a mai tsayuwa matsayin Annabi ga gyãran sha'aninsu, bã ya halatta sai idan akwai wani alhẽria ciki wanda amfaninsa zai shãfi jama'a duka.
( 2 ) Hana fassarar Alƙur'ãni ko sunnar Annabi, ba a kan hanyar da Annabi ko Sahabbansa da waɗanda suka bi hanyarsu suka fassara ba. Da mutum ya yi tãwilin Alƙur'ãni, gãra ya ce bai sani ba. Tãwĩlin Alƙur'ãni ko Hadĩsi da hankali yana kai ga bũɗe ƙõfar kãfirci ɓõyayye da yin hukunci da abin da Allah bai saukar ba. Na'am ba a hana ijtihãdi ga abin da ba a sãmi nassi a kansa ba, ko kuma aka sãmi nassi wanda bã bayyananne ba. Jingina ijtihãdi ga ra'ayi ya fi tãwĩlin abin da bai bayyana ba daga Alƙur'ãni ko Hadĩsi, domin ra'ayi ba ya ɓatar dawasu, amma tãwĩli yana ɓatarwa.
( 3 ) Bayãnin shirki da hukunce- hukuncensa da abin da yake ratayuwa da shi. Sanin ma'anarshirki wajibi ne, dõmin a kan tauhĩdi ne aka gina shikãshikan Musulunci,
( 4 ) Rabon Shaiɗan daga kõwane dubu, shi ne ɗari tare da cas'in da tara kamar yadda aka ruwaito a cikin Hadĩsi.
( 5 ) Suna kãtse kunnuwan dabbõbi dõmin su nũna cewa na gumãkansu ne. Sunan mãtã shi ne ga duk abin da ba ya darai, kamar watã itãtuwa duka mãtã ne. Canza halitta kamar tsãgen fuska da fãƙe haƙõra da karkarar gẽmu dõmin neman kyau, duka umurnin Shaiɗan ne.