Hausa translation of the meaning Page No 98

Quran in Hausa Language - Page no 98 98

Suratul Al-Nisa from 122 to 127


122. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, zã mu shigar da su gidãjen Aljanna ( waɗanda ) ƙõramu sunã gudãna a ƙarƙashinsu, sunã mãsu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wãne ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?
123. ( Al'amari ) bai zama gũrace- gũracenku ba, kuma ( 1 ) ba gũrace- gũracen Mutãnen Littãfi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki zã a sãka masa da shi kuma bã zai sãmi wani masõyi ba, baicin Allah, kuma bã zai sãmi mataimaki ba.
124. Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhãli kuwa Yanã mũmini, to, waɗannan sunã shiga Aljanna kuma bã zã a zãlunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabĩ no ba.
125. Kuma wãne ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhãli kuwa yanã mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrãhĩm, Yanã mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Yã riƙi Ibrãhĩm badãɗayi ( 2 ) .
126. Kuma Allah ke da ( 3 ) ( mallakar ) abin da ke cikin sammai da kuma abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã kasance, a dukkan, kõme, Mai kẽwayewa.
127. Sunã yi maka fatawa a cikin sha'anin mãtã. Ka ce: « Allah Yanã bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantãwa a kanku a cikin Littãfi, a cikin sha'anin marãyun mãtã waɗanda ba ku bã su abin da aka rubũta musu ( 4 ) ( na gãdo ) ba, kuma kunã kwaɗayin ku aurẽ su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yãra, da sha'anin tsayuwarku ga marãyu da ãdalci. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah Yã kasance Masani a gare shi. »
( 1 ) Addini bã tatsuniyar baki bane, aiki ne, ko mutum ya yi mugu ya shĩga Wuta, ko kuma ya yi na ƙwarai ya shigaAljanna.
( 2 ) Akwai kwaɗaitarwa ga cẽwa, wanda yake son AllahYa so shi, to sai ya bi aƙĩda da aiki irin na Ibrãhĩma, sai Allah Ya so shi.
( 3 ) Ko da yake Allah Yã riƙi Ibrãhĩma « Khalĩl » watau masõyi, amma bai hana Ibrahĩma ya zama a cikin bãyin Allah kuma mulkinSa ba, domin yana daga cikin abin da sama daƙasa suka ƙunsa a cikinsu.
( 4 ) A cikin jahiliyya ba su bai wa yãra da mãtã gãdo. Musulunei ya sõke wannan al'ãda daãyar gãdo, ãyã ta 11. Kuma idan akwai wata marainiya gahannun wani tana da dũkiya, sai ya jefa mata mayafinsa domin ya hana ta auren wani namiji. Shi kuma ko ya aure ta ko kuma ya bar ta bãbu aure har ta mutu, su yigãdonta.