Hausa translation of the meaning Page No 104

Quran in Hausa Language - Page no 104 104

Suratul Al-Nisa from 163 to 170


163. Lalle ne Mu, Mun ( 1 ) yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nũhu da annabãwa daga bãyansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrãhĩma da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Yaƙũbu da jĩkõki da ĩsa da Ayũba da Yũnusa da Hãruna da Sulaimãn. Kuma Mun bai wa Dãwũda zabũra.
164. Da wasu Manzanni, haƙĩ ƙa, Mun bã da lãbarinsu a gare ka daga gabãni, da wasu manzanni waɗanda ba Mu bã da lãbãrinsu ba a gare ka, kuma Allah Yã yi magana da Mũsã, magana sõsai.
165. Manzanni mãsu bãyar da bushãra kuma mãsu gargaɗi dõmin kada wata hujja ta kasance ga mutãne a kan Allah bãyan Manzannin. Kuma Allah yã kasance Mabuwãyi, Mai hikima.
166. Amma Allah Yanã shaida da abin da Ya saukar zuwa gare ka. Yã saukar da shi da saninSa. Kuma malã'iku sunã shaida. Kuma Allah Yã isa Ya zama shaida.
167. Lalle ne, waɗanda suka kãfirta kuma suka kange ( wasu mutãne ) daga hanyar Allah, haƙĩƙa, sun ɓace, ɓata mai nĩsa.
168. Lalle ne waɗanda suka kãfirta, kuma suka yi zãlunci, Allah bai kasance Yana yi musu gãfara ba, kuma bã Ya shiryar da su ga hanya.
169. Fãce hanyar Jahannama, sunã mãsu dawwama a cikinta har abada, kuma wannan yã kasance, ga Allah, mai sauƙi.
170. Yã kũ mutãne! Haƙĩƙa, Manzo yã je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Sabõda haka ku yi ĩmãni yã fi zama alhẽri a gare ku. Kuma idan kun kãfirta, to, Allah Yanã da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Yã kasance Masani, Mai hikima.
( 1 ) Muhammadu bã shi ne farkon manzanni ba, kuma bã shi ne aka fãra yi wa wahayi ba, bã shi ne aka fãra bai wa Littãfi ba. Sai dai shi ne ƙarshensu ga dukkan waɗannan abũbuwa, kamar yadda bushãrarsu ta bayyana tun a gabãninsa. Kuma yawan Annabãwa da Manzanni bãbu wanda ya san shi sai Allah, wahayi shi ne ishãra ko yanda Allah ke aiko malã'iki da Manzanci zuwa ga wani Annabi ko Manzonsa.