Hausa translation of the meaning Page No 106

Quran in Hausa Language - Page no 106 106

Suratul Al-Nisa from 176 to 2


176. Sunã yi maka fatawa. ( 1 ) Ka ce: « Allah Yanã bayyana muku fatawa a cikin 'Kalãla. » ' Idan mutum ya halaka, ba shi da, rẽshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gãdon ta, idan wani rẽshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ( 'yan'uwa mãtã ) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mãtã to namiji yana da misãlin rabon mãtã biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, dõmin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kõme.
Sũratul Mã’ida
Tana karantar da cikãwar alkawurra da abin da ya rãtaya da su wajen rarrabewa a tsakãnin halal da haram, da kyautata aƙĩda da aiki.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! ku cika alkawurra. An halatta muku dabbobin jin dãɗi fãce abin da ake karantãwa a kanku, bã kunã mãsu halattar da farauta ba alhãli kuwa kunã mãsu harama. Lalle ne, Allah Yanã hukunta abin da yake nufi.
2. Ya kũ waɗanda suka yi ĩmãni! kada ku halattar da ayyukan ibãdar Allah game da hajji, kuma da watã mai alfarma, kuma da hadaya, kuma da rãtayar raƙuman hadaya, kuma da mãsu nufin Ɗãki mai alfarma, sunã neman falala daga Ubangijinsu da yarda. Kuma idan kun kwance harama, to, ku yi farauta. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutãne ta ɗauke ku, dõmin sun kange ku daga Masallãci Mai alfarma, ga ku yi zãlunci. Kuma ku taimaki junã a kan aikin ƙwarai da taƙawa. Kuma kada ku taimaki juna a kan zunubi da zãlunci, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
( 1 ) Bãyan dõgon bayãni a kan tauhĩdin Allah, da kõrẽwar shubhõhin yahũdu da nasãra a cikin addĩni, dõmin sai zũciya tã yarda da kaɗaitar Allah sa'annan zã ta ji ƙarfin riƙo da ƙarfin ɗauka ga hukunce- hukuncen da Allah Ya ke azã mata. To, yã kõma ne ga abin karantãwar sũrar na tsaron dũkiyã, ya rufe ta da shi. Ya yi magana akan mas'alar 'kalãla', watau, mutum ya mutu bai bar rẽshen sa ba, ko wani asali mai fukã- fukai kawai, watau 'yan uwa maza ko mãta waɗanda ba li'ummaiba. Maganã akan li'ummai kuwa tã gabãta a farkon sũra. Anã gabãtar da shaƙĩƙi a kan li'abi, kuma ana gabãtar da na kusa akan na nesa, mafi kusantar zumunta. Ana ƙiyasin baiawa 'yã'yã mãtã biyu, biyu daga uku na dũkiya akan 'yan uwa mãtã, dõmin su ba a ce fiye da biyu ba. Ɗiyar tsatso ta fi 'yar'uwa ƙarfin zumunta, kuma ta fi kusanci.