Hausa translation of the meaning Page No 108

Quran in Hausa Language - Page no 108 108

Suratul Al-Ma'idah from 6 to 9


6. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni ! idan kun tãshi ( 1 ) zuwa ga salla, to, ku wanke fuskõkinku da hannuwanku zuwa ga magincirõri, kuma ku yi shãfa ga kãnunku, kuma ku ( wanke ) ƙafãfunku zuwa idãnun sãwu biyu. Kuma idan kun kasance mãsu janaba, to, ku yi tsarki, kuma idan kun kasance majinyata, kõ kuwa a kan tafiya, kõ kuwa ɗaya daga gare ku ya zo daga kãshi, kõ kuka yi shãfayyar junã da mãtã, sa'an nan ba ku sãmi ruwa ba to ku yi nufin wuri ( 2 ) mai kyau, sa'an nan ku yi shãfa ga fuskõkinku da hannuwanku daga gare shi. Allah bã Ya nufi dõmin Ya sanya wani ƙunci a kanku, kuma amma Yanã nufi dõmin Ya cika ni'imarSa a kanku, tsammãninku kunã gõdewa.
7. Kuma ku tuna ni'imar Allah akanku da alkawarinku wanda Ya ɗaure ku da shi, a lõkacin da kuka ce: « Mun ji kuma mun yi ɗã'a Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle ne Allah Masani ne ga abin da ke a cikin zukata. »
8. Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayin daka dõmin Allah mãsu shaida da ãdalci. Kuma kada ƙiyayya da wasu mutane ta ɗauke ku a kan bã zã ku yi ãdalci ba. Ku yi ãdalci Shĩ ne mafi kusa ga taƙawa. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Masani ne ga abin da kuke aikatãwa.
9. Allah Yã yi wa'adi ga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Sunã da wata gãfara da lãda mai girma.
( 1 ) Abin da ake halatta salla da shi ruwa mai tsarki domin ɗauke hadasi ƙarami da alwala, da hadasi babba da wanka. ldan bãbu ruwa a yi taimama da wuri na fuskar ƙasa wanda bai sãke ba da wata sana'ar mutum. Bauli da wadiyyi da kãshi da tusa da shãfar jin dãɗi na namiji ga mace ko mace ga namiji, da shafar zakarin kansa, duka suna wajabtar da alwalla. fitar maniyyi da haila suna wajabtar da wanka. Maziyyi na wajabtar da wanke dukkan zakari sa'an nan a yi alwalla. Yankan hannun ɓarãwo yã nuna iyaka inda ake shãfar farilla na taimama, da sunna, kamar yadda ake yin sauran ayyuka duka a kan ƙiyãsinsu bisa ga wasu.
( 2 ) Wãtau ku yi taimama.