Hausa translation of the meaning Page No 109

Quran in Hausa Language - Page no 109 109

Suratul Al-Ma'idah from 10 to 13


10. Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryatã, game da ãyõyinMu, waɗannan su ne abõkan wuta.
11. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lõkacin da wasu mutãne suka yi niyyar su shimfiɗa hannuwansu zuwa gare ku ( 1 ) sai Ya kange hannuwansu daga gare ku, kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma sai muminai su dogara ga Allah kawai.
12. Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu ( 2 ) daga gare su kuma Allah Ya ce: « Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna ( waɗanda ) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya. »
13. To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa.
( 1 ) Wannan kiyãyewa ya auku awurãre da yawa tun Musulmi suna da rauni kuma kãfirai suna da ƙarfi, kuma suna son su kashe Musulmi da Musulunci. Allah Ya tsare su. Saboda haka yanzu da Musulmi suka yi ƙarfi da ƙarfin Allah, yã wajaba a kansu su godewa Allah da taƙawa. watau su riƙe alkawarin Allah, su yi abin da Ya aza musugwargwadon hãli.
( 2 ) An ayyana wakilai goma shabiyu daga ƙabĩlun Bani Isrãĩla goma sha biyu domin su ɗaukar musu alkawari dagawurin, kuma su tsare mutãnensu ga ganin ba a sãɓa wa alkawarin ba. An gina addinin Bani Isrãĩla a kan ƙabĩlanci. Saboda haka addininsu bã ya fita daga dã'irarsu.