Hausa translation of the meaning Page No 12

Quran in Hausa Language - Page no 12 12

Suratul Al-Baqarah from 77 to 83


77. Shin, kuma bã su sanin cẽwa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓõyẽwa da abin da suke bayyanãwa?
78. Kuma daga cikinsu akwai ummiyyai, bã su da sanin Littãfi, fãce tãtsuniyoyi, kuma sũ bã kõme suke yi ba fãce suna yin zato.
79. To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubũta littãfi da hannuwansu sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, dõmin su sayi kuɗi kaɗan da shi, san nan bone ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubũtãwa, kuma bone ya tabbata a gare su daga abin da suke sanã'antãwa.
80. Kuma suka ce: « Wuta bã zã ta shãfe mu ba, fãce, 'yan kwãnuka ƙidãyayyu. » Ka ce: « Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah, sa'an nan Allah ba zai sãɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah? »
81. Na'am! Wanda ya yi tsiwur- wurin mũgun abu, kuma laifinsa ya kẽwaye shi, to, waɗannan su ne 'yan Wuta, sũ a cikinta madawwama ne.
82. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, sũ a cikinta madawwama ne.
83. Kuma a lõkacin da Muka karɓi alkawarin Bani- Isrã'ĩla ( 1 ) : « Kada ku bauta wa kõwa fãce Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata, da mai zumunta da marãyu da matalauta, kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutãne, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bãyar da zakka, sa'an nan kuka jũya bãya, fãce kaɗan daga gare ku,alhãli kuwa kuna mãsu bijirẽwa. »
( 1 ) Tunãtar da Banĩ Isrã'ĩla alkawurra gõma da Allah Yã yi da Mũsã a cikin Attaura a kansu. Na farko bã zã su bauta wa kõwa ba fãce Allah. Na biyu kyautata wa iyãye da dangi da marãyu da matalauta. Na uku, faɗin magana mai kyau zuwa ga mutãne. Na huɗu, tsayar da salla. Nabiyar, bãyar da zakka. Na shida, bã zã a kashe rai bãbu hakki na sharĩ'a ba. Na bakwai, bã zã a fitar da kõwa daga gidansa ba. Na takwas, bã zã a taimaki azzãlumi a kan zãluncinsa ba. Na tara, idan abõkan gãbã sun kãma wani daga cikinsu, su yi fansarsa. Nagõma, ɗã'a ga kõwane Manzon Allah wanda bai sãɓãwa Attaura ba ga aƙida.