Hausa translation of the meaning Page No 13

Quran in Hausa Language - Page no 13 13

Suratul Al-Baqarah from 84 to 88


84. Lõkacin da Muka riƙi alkawarinku; bã zã ku zubar da jininku ba, kuma bã zã ku fitar da kanku daga gidãjenku ba; sa'an nan kuka tabbatar alhãli kuwa kuna bãyar da shaida ( a kanku ) .
85. Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci ( 1 ) a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar Ƙiyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa.
86. Waɗannan su ne waɗanda suka sayi rãyuwar dũniya da Lãhira, dõmin haka bã zã a sauƙaƙa azãba ba daga kansu, kuma sũ, bã ataimakonsu.
87. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Munbai wa Mũsã Littãfi, kuma Mun biyar daga bãyansa da wasu Manzanni, kuma Muka bai wa Ĩsã ɗan Maryama hujjõji bayyanannu, kuma Muka ƙarfafa shi da Rũhi mai tsarki. ( 2 ) Shinfa, kõ da yaushe wani manzo ya je muku tãre da abin da rãyukanku bã su so, sai ku kangara, wani ɓangare kun ƙaryata, kuma wani ɓangare kuna kashẽwa?
88. Kuma suka ce: « Zukatanmu suna cikin rufi. » A'a, Allah Yã la'ane su, dõmin kafircinsu kadan kwarai suke yin ĩmãni!
( 1 ) Aiki da sãshen wasu abũbuwa na addini da barin wasu kãfirci ne mai wajabta wulãƙanci a kan Musulmi.
( 2 ) Rũhul Kuds; watau ran tsarki kõ rai mai tsarki, shi ne Jibirilu, amincin Allah ya tabbata a gare Shi. Ya zauna tãre da Ĩsã inda duk yake sunã tãre. Ãyõyin da aka bai wa Ĩsã sũ ne rãyar da matattu da warkar da kutãre da makãfi da marasa lãfiya. Wannan ya sanyacẽwa mãsu da'awar bin sa suka fito da aikin maristan, watau asibiti.