Hausa translation of the meaning Page No 120

Quran in Hausa Language - Page no 120 120

Suratul Al-Ma'idah from 71 to 76


71. Kuma suka yi zaton cewa wata fitina bã zã ta kasance ba sai Suka makanta, kuma suka kurubta, sa'an nan Allah Ya karɓi tuba a gare su, sa'an nan suka makanta kuma suka kurunta mãsu yawa daga gare su, alhãli Allah Mai gani ne ga abin da suke aikatãwa.
72. Lalle ne haƙĩƙa waɗanda ( 1 ) suka ce: « Lalle ne Allah, shĩne Masĩhu, ɗan Maryama, » sun kãfirta. Alhãli kuwa Masĩhu yã ce: « Yã Banĩ Isrã'ĩla! Ku bauta wa Allah Ubangijina, kuma Ubangijinku. » Lalle ne shĩ, wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne, Allah Yã haramta masa Aljanna. Kuma bãbu wasu mataimaka ga azzãlumai.
73. Lalle ne, haƙĩƙa, waɗanda suka ce: « Allah na ukun uku ne, » sun kãfirta, kuma babu wani abin bautãwa fãce Ubangji Guda. Kuma idan ba su hanu daga abin da suke faɗa ba, haƙĩƙa, wata azãba mai raɗaɗi tãnã shãfar waɗanda suka kãfirta daga gare su.
74. shin fã, bã su tuba zuwa ga Allah, kuma su neme Shi gãfara, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai?
75. Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa, kuma uwarsa siddika ( 2 ) ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi. Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su.
76. Ka ce: « Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani ( 3 ) alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani? »
( 1 ) Su ne Ya'aƙũbiyya, Bãyan bayãni a kan aibõbin Yahũdu sai Ya shiga bayãni a kan aibõbin Nasãra.
( 2 ) Siddĩƙ shi ne mai yawan gaskatãwar Annabãwa, shi ne mafi ɗaukakar daraja a waliyyan Allah, kamar Abubakar siddĩƙ Sahãbin Annabi.
( 3 ) Idan bauta wa Ĩsã, Annabin Allah ya zama kãfirci bauta wa waliy yã zama shirka kenen. Kuma idan Ĩsã bai mallaki kõme ba, to, waliyyi mene ne matsayinsa?