Hausa translation of the meaning Page No 121

Quran in Hausa Language - Page no 121 121

Suratul Al-Ma'idah from 77 to 82


77. Ka ce: « Yã ku Mutanen Littãfi! Kada ku zurfafa a cikin addininku, abin da bã gaskiya ba, kuma kada ku bĩbiyi son zuciyõyin waɗansu mutãne waɗanda suka riga suka ɓace a gabãni, kuma suka ɓatar da wasu mãsu yawa, kuma suka ɓace daga tsakar hanya. »
78. An la'ani waɗanda suka kãfirta daga Banĩ Isrã'ĩla a kan harshen Dãwuda da Ĩsa ɗan Maryama. wannan kuwa sabõda sãɓãwar da suka yi ne, kuma sun kasance suna ta'addi ( 1 ) .
79. Sun kasance bã su hana juna daga abin ƙi, wanda suka aikata. Haƙĩƙa abin da suka kasancesunã aikatãwa yã munana.
80. Kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã jiɓintar waɗanda suka kãfirta. Haƙĩƙa tir da abin da rãyukansu suka gabãtar sabõda su, watau Allah Yã yi fushi da su, kuma a cikin azãba su mãsu dawwama ne
81. Kuma dã sun kasance sunã ĩmãni da Allah da Annabi da abin da aka saukar zuwa gare shi, dã ba su riƙe su masõya ba. Kuma amma mãsu yawa daga gare su, fãsiƙai ne.
82. Lalle ne kana sãmun mafiya tsananin mutãne a adãwa ga waɗanda suka yi ĩmãni,Yahudu ne da waɗanda suka yi shirki. Kuma lalle ne kanã sãmun mafiya kusantarsu a sõyayya ga waɗanda suka yi ĩmãni su ne waɗanda suka ce: « Lalle mu ne Nasãra. » Wancan kuwa sabõda akwai Ƙissawa da ruhubãnãwa ( 2 ) daga cikinsu. Kuma lalle ne su, bã su yin girman kai.
( 1 ) Ta'addi shĩ ne ƙetare iyãka da nufin zãlunci.
( 2 ) Ƙissĩsi shĩ ne lĩmãnin kiristãwa, ruhubãnanci shĩ ne mutum ya tsabbace daga mutãne dõmin ibãda, kuma ba ya yin aure. Baruhubãne guda, ruhubãnãwa jam'i.