Hausa translation of the meaning Page No 138

Quran in Hausa Language - Page no 138 138

Suratul Al-An'am from 82 to 90


82. « Waɗanda suka yi ĩmãni, kuma ba su gauraya ĩmãninsu da zãlunci ba, waɗannan sunã da aminci, kuma sũ ne shiryayyu. »
83. Kuma waccan ita ce hujjarMu, Mun bayãr da ita ga Ibrãhĩma a kan mutãnensa. Munã ɗaukaka wanda Muka so da darajõji. Lalle ne Ubangijinka Mai hikima ne, Masani.
84. Kuma Muka bã shi Is'hãƙa da Yãƙubu, dukansu Mun shiryar, kuma Nũhu Mun shiryar da shi a gabãni, kuma daga zuriyarsa akwai Dãwũda da Sulaimãnu da Ayyũba, da Yũsufu da Mũsã da Hãrũna, kuma kamar wancan ne Muke sãka wa mãsu kyautatãwa.
85. Da Zakariyya da Yahaya da Isa da Ilyasu dukansu daga sãlihai suke.
86. Da Ismã'la da Ilyasa, a da Yũnusa da Luɗu, kuma dukansu Mun fĩfĩtã su a kan tãlikai.
87. Kuma daga ubanninsu, da zũriyarsu, da 'yan'uwansu, kuma Muka zãɓe su, kuma Muka shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya.
88. Wancan ne shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Yake so daga bayinSa. Kuma dã sun yi shirki dã haƙĩƙa abin da suka kasance sunã ,aikatãwa yã lãlãce.
89. Waɗancan ne waɗanda Muka bai wa Littãfi da hukunci da Annabci. To idan waɗannan ( mutãne ) sun kãfirta da ita, to, haƙĩƙa, Mun wakkala wasu mutãne gare ta, ba su zama game da ita kãfirai ba.
90. Waɗancan ne Allah Ya shiryar, sabõda haka ka yi kõyi da shiryarsu. Ka ce: « Ba ni tambayar ku wata ijãra. Shĩ ( Alƙur'ãni ) bai zama ba fãce tunãtarwa ga tãlikai. »