Hausa translation of the meaning Page No 146

Quran in Hausa Language - Page no 146 146

Suratul Al-An'am from 138 to 142


138. Kuma sukace: « Waɗannan dabbõbi da shũka hanannu ne; bãbu mai ɗanɗanar su fãce wanda muke so, » ga riyãwarsu. Da wasu dabbõbi an hana bãyayyakinsu, da wasu dabbõbi bã su ambatar sũnan Allah a kansu, bisa ƙirƙiren ƙarya gare Shi. Zai sãka musu da abin da suka kasance sunã ƙirƙirãwa.
139. Kuma suka ce: « Abin da yake a cikin cikkunan waɗannan dabbõbi kẽɓantacce ne ga mazanmu, kuma hananne ne a kan mãtan aurenmu. Kuma idan ya kasance mũshe, to, a cikinsa sũ abõkan tãrayya ne, zai sãka musu sifantãwarsu. Lalle ne Shĩ, Mai hikima ne, Masani. »
140. Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba.
141. Kuma Shĩ ne Wanda Ya ƙãga halittar gõnaki mãsu rumfuna da wasun mãsu rumfuna da dabĩnai da shũka, mai sãɓãwa ga 'yã'yansa na ci, da zaituni da rummãni mai kama da jũna da wanin mai kama da jũna. Ku ci daga 'ya'yan itãcensa, idan ya yi 'yã'yan, kuma ku bãyar da hakkinSa a rãnar girbinsa, kuma kada ku yi ɓarna. Lalle ne Shĩ, ba Ya son mafarauta.
142. Kuma daga dabbõbi ( Ya ƙãga halittar ) mai ɗaukar kãya da ƙanãna; Ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku, kuma kada ku bi zambiyõyin shaiɗan: LalLe ne shi, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne.