Hausa translation of the meaning Page No 147

Quran in Hausa Language - Page no 147 147

Suratul Al-An'am from 143 to 146


143. Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya.
144. Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai.
145. Ka ce: « Bã ni sãmu, ( 1 ) a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi. » Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
146. Kuma a kan waɗanda suka tũba ( Yahũdu ) Mun haramta ( 2 ) dukan mai akaifa, kuma daga shãnu da bisãshe Mun haramta musu kitsattsansu fãce abin da bãyukansu suka ɗauka, kõ kuwa kãyan ciki, kõ kuwa abin da ya garwaya da ƙashĩ wannan ne Muka sãka musu sabõda zãluncinsu, kuma Mu, haƙĩƙa, Mãsu gaskiya ne.
( 1 ) Bayãnin abũbuwan da aka haramta cinsu daga dabbõbi waɗanda Allah Ya hana, bã waɗanda al'ãda ta hana ba.
( 2 ) Bayãnin abũbuwan da Allah Ya hana a kan Yahũdu, shi ma hanin an yĩ shi sabõda wani laifinsu ne.