Hausa translation of the meaning Page No 145

Quran in Hausa Language - Page no 145 145

Suratul Al-An'am from 132 to 137


132. Kuma ga kõwanne, ( 1 ) akwai darajõji daga abin da suka aikata. Kuma Ubangijinka bai zama mai shagala ba daga abin da suke aikatãwa.
133. Kuma Ubangijinika Wadãtacce ( 2 ) ne Ma'abũcin rahama. Idan Yã so zai tafi da ku, kuma Ya musanya daga bãyanku, abin da Yake so, kamar yadda Ya ƙãga halittarku daga zũriyar wasu mutãne na dabam.
134. Lalle ne abin da ake yi muku wa'adi lalle mai zuwa ne kuma ba ku zama mãsu buwãya ba,
135. Ka ce: « Yã ku mutãnena! Ku yi aiki a kan halinku, lalle ne nĩ mai aiki ne, sa'an nan da sannu zã ku san wanda ãƙibar gida zã ta kasance a gare shi. Lalle ne shi, azzãlumai bã zã su ci nasarã ba. »
136. Kuma sun sanya wani rabõ ga Allah daga abin da Ya halitta daga shũka da dabbõbi, sai suka ce: « Wannan ( 3 ) na Allah ne, » da riyãwarsu « Kuma wannan na abũbuwan shirkinmu ne. » Sa'an nan Abin da ya kasance na abũbuwan shirkinsu, to, bã ya sãduwa zuwa Allah, kuma abin da ya kasance na Allah, to, shĩ yanã sãduwa zuwa ga abũbuwan shirkinsu. Tir da hukuncinsu!
137. Kuma kamar wancan ne abũbuwan shirkinsu suka ƙãwata wa mãsu yawa, daga mãsu shirkin; kashewar ( 4 ) 'ya'yansu, dõmin su halaka su kuma dõmin su rikitar da addininsu a gare su, Kuma dã Allah Yã so dã ba su aikatã shi ba. Sabõda haka ka bar su da abin da suke ƙirƙirãwa.
( 1 ) Kõwace jama'a, ta mãsu ɗã'a da ta mãsu sabõ, sunã da sakamakõ gwargwadon matsayin kõwanne, ga ĩmãninsa da aikinsa kõ kuwa kãfircin sãɓonsa.
( 2 ) Rashin gaugãwar yin sãkamako ga mãsu laifi sabõda wadãtar Allah ne. Bã shi yin uƙũba dõmin Ya yi fushin an rage masa mulki, haka kuma bã shi yin ni'imadõmin an ƙãra masa mulki. Sai dai dõmin Ya nũna ãdalci da falala ne kawai.
( 3 ) Sun kasance a cikin jãhiliyyaidan suka yi nõma kõ kuwa idan suka sãmi' yã'yan itãce, sai su sanya wani juz'i daga gare shi ga Allah, wani juz'i kuma ga gumãka. Abin da yake rabon gumaka, sai su tsare shi, kuma su lissafce shi. Idan wani abu ya fãɗi dagaabin da aka ambace shi ga samad, sai su mayar da shi zuwa ga rabõn gumãka, amma rabõn gumãkan, bã ya zuwa ga na Allah. Anã bayãr da rabon Allah ga miskĩnai, kuma rabõn gumaka ga matsaransu.
( 4 ) Sunã turbuɗe 'ya'ya mata, dõmin tsõron talauci kõ dõmin tsõron kunya. Sai mai haihuwa ta haihu a bãkin rãmi, idan mace ta haifa, sai ta tũra ta cĩkin rãmin ta rufe, idan kuma namiji ne sai ta bar shi. Haka kuma kashe 'ya'ya, a kan bãkance da alwãshi, sunã ganin sa ibada ne.