Hausa translation of the meaning Page No 149

Quran in Hausa Language - Page no 149 149

Suratul Al-An'am from 152 to 157


152. Kada ku kusanci dũkiyar marãya fãce da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga ƙarfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikẽli da ãdalci, bã Mu kallafã wa rai fãce iyãwarsa. Kuma idan kun faɗi magana, to, ku yi ãdalci, kuma ko dã yã kasance ma'abũcin zumunta ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi: Tsammãninku, kunã tunãwa.
153. Kuma lalle wannan ne tafarkĩNa, yana madaidaici: Sai ku bĩ shi, kuma kada ku bi wasu hanyõyi, su rarrabu da ku daga barin hanyãTa. Wannan ne Allah Ya yi muku wasiyya da shi tsammãninku, kunã yin taƙawa.
154. Sa'an nan kuma Mun bai wa Mũsã Littãfi, yanã cikakke bisa ga wanda ya kyautata ( hukuncin Allah ) da rarrabẽwa, daki- daki, ga kõwane abu, da shiriya da rahama, tsammãninsu, ( 1 ) sunã yin ĩmãni da haɗuwa da Ubangijinsu.
155. Kuma wannan Littãfi ne, Mun saukar da shi, mai albarka ne, sai ku bĩ shi kuma ku yi taƙawa, tsammãninku, anã jin ƙanku.
156. ( Dõmin ) kada ku ce: « Abin sani kawai, an saukar da littãfi a kan ƙungiya ( 2 ) biyu daga gabãninmu, kuma lalle ne mũ, mun kasance, daga karatunsu, haƙĩƙa, gãfilai. »
157. Kõ kuwa ku ce: « Dã dai lalle mũ an saukar da Littãfi a kanmu, haƙĩƙa, dã mun kasance mafiya,shiryuwa daga gare su. » To, lalle ne wata hujja bayyananniya, daga Ubangijinku, tã zo muku, da shiriya da rahama. To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙaryata game da ãyõyin Allah, kuma ya finjire daga barinsu? Zã Mu sãka wa waɗanda suke finjirẽwa daga barin ãyõyinMu da mugunyar azãba, sabõda abin da suka kasance sunã yi na hinjirẽwa.
( 1 ) Mabiya Littãfin Mũsã watau Yahũdu, idan sun san cẽwa Alƙur'ãni kamar Attaura yake daga Allah aka saukar da shi, kuma Muhammadu Annabin Allah ne kamar Mũsã kuma sũduka suna gaskata jũnã, sai su ji sauƙin ĩmãni da shi.
( 2 ) Ana magana da mãsu shirkinLãrabãwa, ƙungiyõyin biyu kuwa su ne Yahũdu da Nasãra, littãfin shĩ ne Attaura da Linjĩla.