Hausa translation of the meaning Page No 151

Quran in Hausa Language - Page no 151 151

Suratul Al-A'raf from 1 to 11


Sũratul A‘rãf
Tanã karantar da tsẽre a tsakãnin gaskiya da ƙarya, tun farko, kuma hãlin ba zai gushe ba yanã a kan haka, har Tãshin Sã’a.
Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.
1. A. L̃. M̃. Ṣ̃.
2. Littãfi ne aka saukar zuwa gare ka, kada wani ƙunci ya kasance a cikin ƙirjinka daga gare shi, dõmin ka yi gargaɗi da shi. Kuma tunãtarwa ne ga mũminai.
3. Ku bi abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, kuma kada ku dinga bin wasu majiɓinta baicinSa. Kaɗan ƙwarai kuke tunãwa.
4. Kuma da yawa wata alƙarya Muka halaka ta, sai azãbarMu ta jẽ mata da dare kõ kuwa sunã mãsu ƙailũla.
5. Sa'an nan bãbu abin da yake da'awarsu, a lõkacin da azãbarMu ta jẽ musu, fãce suka ce: « Lalle ne mũ muka kasance mãsu zãlunci, »
6. Sa'an nan lalle ne Munã tambayar waɗanda aka aika zuwa gare su, kuma lalle Munã tambayar Manzannin.
7. Sa'an nan haƙĩƙa Munã bã su lãbãri da ilmi kuma ba Mu kasance mãsu fakowa ba.
8. Kuma awo a rãnar nan ne gaskiya. To, wanda sikẽlansasuka yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu cin nasara.
9. Kuma wanda sikẽlansa suka yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu, sabõda abin da suka kasance, da ãyõyinMu, sunã yi na zãlunci.
10. Kuma lalle ne haƙĩƙa, Mun sarautar da ku, a cikin ƙasa, kuma Mun sanya muku abũbuwan rãyuwa, a cikinta; kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa.
11. Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halittã ku sa'an nan kuma Mun sũrantã ku, sa'an nan kumaMun ce wa malã'iku: « Ku yi sujada ga Ãdam. » Sai suka yi sujada fãce Iblĩs, bai kasance daga mãsuyin sujadar ba. ( 1 )
( 1 ) Allah Yã ƙidanya ni'imõmin da Ya yi wa mutãne daga halittarsu da sũrantã su da Ya yi kuma Ya girmama su da sanyãwar malã'iku su yi sujada ga ubansu Ãdam, sa'an nan kuma Ya nũna musu cẽwa shaiɗan yã ƙi bin umurninSa ga girmama ubansu Ãdam, sabõda haka sũ ma su yi tsõron maƙiyin kãkansu.