Hausa translation of the meaning Page No 152

Quran in Hausa Language - Page no 152 152

Suratul Al-A'raf from 12 to 22


12. Ya ce: « Mẽne ne ya hana ka, ba ka yi sujada ba, alõkacin da Na umurce ka? » Ya ce: « Nĩ ne mafĩfĩci daga gare shi, Ka halitta ni daga wuta alhãli kuwa Kã halitta shi daga lãka. »
13. Ya ce: « To, ka sauka daga gare ta; dõmin bã, ya kasancẽwa a gare ka ga ka yi girman kai a cikinta. Sai ka fita. Lalle ne kanã daga mãsu ƙasƙanci. »
14. Ya ce: « Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar ( 1 ) da su. »
15. Ya ce: « Lalle ne, kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri. » ( 2 )
16. Ya ce: « To inã rantsuwa da halakarwar da Ka yi mini, lalle ne, inã zaune musu tafarkinKa madaidaici. »
17. « Sa'an nan kuma haƙĩƙa, Inã je musu daga gaba gare su, kuma daga bãya gare su, kuma daga jihõhin damansu da jihõhin hagunsu; Kuma bã zã ka sãmi mafi yawansu mãsu gõdiya ba. »
18. Ya ce: « Ka fita daga gare ta kanã abin zargi kõrarre. Lalle ne wanda ya bĩ ka daga gare su, haƙĩƙa, zã Ni cika jahannama daga gare ku, gabã ɗaya. »
19. « Kuma ya Ãdam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci wannan itãciya, har ku kasance daga azzãlumai. »
20. Sai Shaiɗan ya sanya musu waswãsi dõmin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: « Ubangijinku bai hanã ku daga wannan itãciya ba fãce dõmin kada ku kasance malã'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama. »
21. Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, haƙĩƙa, daga mãsu nasĩha ne.
22. Sai ya saukar da su da rũɗi. Sa'an nan a lõkacin da suka ɗanɗani itãciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma suka shiga sunã lĩƙawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: « Shin, Ban hanã ku ba daga waccan itãciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaiɗan, a gare ku, maƙiyi ne bayyananne? »
( 1 ) Yã rõƙi kada ya mutu, dõmin a Rãnar Rãyarwa bãbu sauran wata mutuwa.
( 2 ) wannan ya nũna cẽwa, kõwaya rõki Allah wani abu, to, zai bã shi gwargwadon yaddaYake so, Shi Ubangijin.