Hausa translation of the meaning Page No 155

Quran in Hausa Language - Page no 155 155

Suratul Al-A'raf from 38 to 43


38. Ya ce: « Ku shiga a cikin al'ummai waɗanda, haƙĩƙa, sun shige daga gabãninku, daga aljannu da mutãne, a cikin Wuta. A kõ da yaushe wata al'umma ta shiga sai ta la'ani 'yar'uwarta, har idan suka riski jũna, a cikinta, gabã ɗaya, ta ƙarshensu ta ce wa ta farkonsu: » Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne suka ɓatar da mu, sai Ka kãwo musu azãba ninki daga wuta. « Ya ce: » Ga kõwane ( 1 ) akwai ninki; kuma amma ba ku sani ba. « »
39. Kuma ta farkonsu ta ce wa ta ƙarshe: « To, bã ku da wata falala a kanmu, sai ku ɗanɗana azãba sabõda abin da kuka kasance kunã tãrãwa! »
40. Lalle ne waɗanda suka ƙaryatã game da ãyõyinMu, kuma suka yi girman kai daga barinsu, bã zã a bubbuɗe musu kõfõfin sama ba, kuma bã su shiga Aljanna sai raƙumi ya shiga kafar allũra, kuma kamar wannan ne Muke sãka wa mãsu laifi.
41. Sunã da wata shimfiɗa daga Jahannama kuma daga samansu akwai wasu murafai. Kuma kamar wancan ne Muke sãka wa azzãlumai.
42. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, bã Mu ƙallafa wa rai fãce iyãwarsa, Waɗannan ne abõkan Aljanna, sũ, a cikinta, madawwma ne.
43. Kuma Muka fitar da abin da yake a cikin ƙirãzansu, daga ƙiyayya, ƙõramu sunã gudãna daga ƙarƙashinsu, kuma suka ce: « Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya shiryar da mu ga wannan. Kuma ba mu kasance munã iya shiryuwa ba, bã dõmin Allah Ya shiryar da mu ba. Lalle ne haƙĩƙa, Manzannin Ubangjinmu, sun jẽ mana da gaskiya. » Kuma aka kira su, cẽwa: « Waccan Aljlnna an gãdar da ku ita, sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa. »
( 1 ) Shũgabannin ɓata su ne ke fãra shiga wuta, sa'an nan mabiyansu, su shiga, dõmin shũgabanni snnã da laifi biyu; nãsu, na aikinsu, da kuma sababin da suka yi, na ɓatar da mabiyansu. Kuma an fahimta daga nan cẽwa, « Inã bin wãnea kan ɓata, shĩ ne ya ɓatar da ni, bã ya zama hujja mai hana shiga wuta, dõmin AllahYã aza wa kõwane bãligi mai hankali da yayi binciken gaskiya gwargwadon iyãwarsa. Allah ba Ya kãma mutum da abin da ba ya a cikin ĩkonsa.»