Hausa translation of the meaning Page No 156

Quran in Hausa Language - Page no 156 156

Suratul Al-A'raf from 44 to 51


44. Kuma 'yan Aljanna suka kirãyi 'yan Wuta suka ce: « Lalle ne mun sãmi abin da Ubangijinmu Ya yi mana wa'adi, gaskiya ne. To, shin, kun sãmi abin da Ubangijinku Ya yi muku wa'adi, gaskiya? » Suka ce: « Na'am. » Sai mai sanarwa ya yi yẽkuwa, cẽwa: « La'anar Allah ta tabbata a kan azzãlumai. »
45. « Waɗanda suke kangẽwa daga hanyar Allah, kuma sunã nẽman ta ta zama karkatacciya,. kuma sũ, game da Lãhira, kãfirai ne. »
46. Kuma a tsakãninsu akwai wani shãmaki, ( 1 ) kuma a kan A'arãf akwai wasu maza sunã sanin kõwa da alãmarsu; Kuma suka kirãyi abõkan Aljamia cẽwa: « Aminci ya tabbata a kanku: » Ba su shige ta ba, alhãli kuwa sũ, sunã tsammãni.
47. Kuma idan an jũyar da gannansu wajen abõkan wuta, su ce: « Yã Ubangijinmu! Kada Ka sanyã mu tãre da mutãne azzãlumai. »
48. Kuma abõkan A'araf suka kirãyi wasu maza, sunã sanin su da alãmarsu, suka ce: « Tãrawar dũkiyarku da abin da kuka kasance kunã yi na girman kai, bai wadãtar ba daga barinku? »
49. « Shin, waɗannan ne waɗanda kuka yi rantsuwa, Allah bã zai sãme su da rahama ba? Ku shiga Aljanna, bãbu tsõro akanku, kuma ba ku zama kunã baƙin ciki ba. »
50. Kuma 'yan wuta suka kirãyi 'yan Aljanna cẽwa: « Ku zubo a kaumu daga ruwa kõ kuwa daga abin da Allah Ya azurta ku. » Su ce: « Lalle ne Allah Ya haramtã su a kan kãfirai. »
51. « Waɗanda suka riƙi addininsu abin shagala da wãsa, kuma rãyuwar dũniya ta rũɗe su. » To, a yau Munã mantãwa da su, kamar yadda suka manta da haɗuwa da yininsu wannan, da kuma abin da suka kasance da ãyoyinMu sunã musu.
( 1 ) A tsakanin Aljanna da wuta akwai bango, anã ce masa A'araf, inda zã a ajiye mutãnenda ayyukansu na ƙwarai suka yi daidai da miyãgun ayyukansu. Sunã ganin mutãnen Aljanna sunã yi musu sallama sunã gurin shigarta, kuma sunã ganin mutãnen wuta sunã la'anar su, sunã nẽman nisantadaga gare ta.