Hausa translation of the meaning Page No 165

Quran in Hausa Language - Page no 165 165

Suratul Al-A'raf from 121 to 130


121. Suka ce: « Mun yi ĩmãni da Ubangijin halittu. »
122. « Ubangijin Mũsã da Harũna. »
123. Fir'auna ya ce: « Ashe, kun yi ĩmãni da shi a gabãnin inyi izni a gare ku? Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, mãkirci ne kuka mãkirta a cikin birni, dõmin ku fitar da mutãnensa daga gare shi; To, da sannu zã ku sani. »
124. « Lalle ne, inã karkãtse hannãyenku da ƙafãfunku daga sãɓãni, sa'an nan kuma, haƙĩƙa, inã tsĩre, ku gabã ɗaya. »
125. Suka ce: « Lalle ne mu, zuwa ga Ubangijinmu, mãsu jũyãwa ne. »
126. « Kuma bã ka zargin kõme daga gare mu fãce dõmin mun yi ĩmãni da ãyõyin Ubangijinmu a lõkacin da suka zõ mana! Ya Ubangijinmu! Ka zuba haƙuri a kanmu, kuma Ka cika mana munã Musulmai! ( 1 ) »
127. Kuma mashawarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: « Shin, zã ka bar Mũsã da mutãnensa dõmin su yi ɓarna a cikin ƙasa, kuma ya bar ka, kai da gumãkanka? » Ya ce: « Zã mu yayyanka ɗiyansu maza kuma mu rãya mãtansu; kuma lalle ne mũ, a bisa gare su, marinjãya ne. »
128. Mũsã ya ce wa mutãnensa: ( 2 ) « Ku nẽmi taimako da Allah, kuma ku yi haƙuri; Lalle ne ƙasa ta Allah ce, Yãna gãdar da ita ga wanda Yake so daga bãyinSa, kuma ãƙiba ta mãsu taƙawa ce. »
129. Suka ce: « An cũtar da mu daga gabãnin ka zõ mana, kuma daga bãyan da kã zõ mana. » Ya ce: « Akwai tsammãnin Ubangijinku, Ya halaka maƙiyanku, kuma Ya sanya ku, ku maye a cikin ƙasa, sa'an nan Ya dũba yadda kuke aikatãwa. »
130. Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun kãma mutãnen Fir'auna da tsananin shẽkaru ( fari ) da nakasa daga 'ya'yan itãce; Tsammãninsu sunã tunãwa.
( 1 ) Musulmi shi ne wanda ya sallama kansa ga hukunce- hukuncen Allah waɗanda wani Annabin Allah ya zõ da su, a cikin zãmaninsa. Sabõda haka ma'anar Musulmi shi ne mai sallamãwa ga hukuncin Allah, a kõwane zãmani, tun daga Ãdamu har zuwa Rãnar Ƙiyãma. Sai dai wannan al'umma ta Muhammadu tã kẽɓanta da sũnan Musulmi, addinin kuma da sũnan Musulunci.
( 2 ) Maganar Mũsã ga Banĩ Isrã'ila tã nũna cẽwa sun ga azãbar ta yi musu yawa, har sun fãra zargin Mũsã da cẽwa ya sabbaba musu tsananin fitinar, da zõwarsa. Shi kuma ya lallãshe su da cẽwa, « Kõme ya yi tsanani, to, sauƙinsa ya yi kusa. »