Hausa translation of the meaning Page No 164

Quran in Hausa Language - Page no 164 164

Suratul Al-A'raf from 105 to 120


105. « Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni. »
106. Ya ce: « Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya. »
107. Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!
108. Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!
109. Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: « Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi. »
110. « Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa? »
111. Suka ce: « Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa. »
112. « Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi. »
113. Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: « Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya? »
114. Ya ce: « Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta. »
115. Suka ce: « Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa? »
116. Ya ce: « Ku jẽfa. » To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma. « »
117. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: « Ka jẽfa sandarka. » Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!
118. Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.
119. Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.
120. Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada.