Hausa translation of the meaning Page No 166

Quran in Hausa Language - Page no 166 166

Suratul Al-A'raf from 131 to 137


131. Sa'an nan idan wani alhẽri ya jẽ musu, sai su ce: « Masĩfa ta sãme su, sai su yi shu'umci da Mũsã da wanda yake tãre da shi, To, shu'umcinsu a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawansu bã su sani! »
132. Kuma suka ce: « Kõ me ka zõ mana da shi daga ãyã, dõmin ka sihirce mu da ita, to, baza mu zama, sabõda kai, mãsu ĩmãni ba. »
133. Sai Muka aika a kansu da cikõwa, da fãra, da ƙwarƙwata da kwãɗi, da jini; ãyõyi abũbuwan rarrabẽwa; ( 1 ) Sai suka kangare, kuma suka kasance mutãne mãsu laifi.
134. Kuma a lõkacin da masĩfa ta auku a kansu, sukan ce: « Yã Mũsã! Ka rõƙa mana Ubangijinka, sabõda abin da Ya yi alkwari a wurinka, lalle ne idan ka kau da azãbar daga barinmu, haƙĩƙa Munã ĩmãni sabõda kai, kuma munã sakin Banĩ Isrã'ila tĩre da kai. »
135. To, a lõkacin da Muka kuranye azãba daga barinsu zuwa a wani ajali wanda suke mãsu iske shi ne, sai gã su sunã warwarẽwa!
136. Sai Muka yi azãbar rãmuwa, daga gare su, sabõda haka Muka nutsar da su a cikin tẽku, dõmin lalle ne sũ, sun ƙaryata game da ãyõyinMu, kuma sun kasance daga barinsu, gãfilai.
137. Kuma Muka gãdar da mutãnen, waɗanda sun kasance anã raunana su, a gabacin ƙasa da yammacinta, wadda Muka sanya albarka a cikinta, kuma kalmar Ubangijinka mai kyau ta cika a kan Banĩ Isrã'ĩla, sabõda abin dasuka yi na haƙuri. Kuma Muka murtsuke abin da Fir'auna da mutãnensa suka kasance sunã sanã'antawa, da abin da suka kasance sunã shimfiɗãwa. ( 2 )
( 1 ) Ãyõyin da suka jẽ musu a cikin lõkatai daban- daban dõmin a ja hankalinsu, kõ zã su yi ĩmãni. Kõwace ãyã tanã kwãna bakwai sunã wahala da ita, sa'an nan su rõƙi Mũsã ya yi addu'a a kuranye ta, sa'an nan a bãyan wani lõkaci sai su kõma wa kãfircinsu, kamar yadda ãyõyi mãsu biyar wannan suka bayyana.
( 2 ) Wannan shi ne ƙarshen ƙissar faɗan gaskiya daga wajen Mũsã da ƙarya daga wajen Fir'auna da rundunarsa da dũkiyarsa. Haka dai ƙarya kõme duhunta, to, na banzane, a ƙarshe zã ta wãtsa.