Hausa translation of the meaning Page No 178

Quran in Hausa Language - Page no 178 178

Suratul Al-Anfal from 9 to 16


9. A lõkacin da kuke nẽman Ubangijinku tairnako, sai Ya karɓa muku cẽwa: « Lalle ne Nĩ, Mai taimakon ku ne da dubu daga malã'iku, jẽre. »
10. Kuma Allah bai sanya shi ba fãce Dõmin bishãra, kuma dõmin zukãtanku su natsu da shi, kuma taimakon, bai zama ba fãce daga wurin Allah; Lalle ne Allah Mabuwãyi ne, Mai hikima.
11. A lõkacin da ( Allah ) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa ( 1 ) daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi.
12. A lõkacin da Ubangijinka Yake yin wahayi zuwa ga Malã'iku cẽwa: « Lalle ne Ni, Inã tãre da ku, sai ku tabbatar da waɗanda suka yi ĩmãni: Zã Ni jẽfa tsõro a cikin zukãtan waɗanda suka kãfirta, sai ku yi dũka bisa ga wuyõyi kuma ku yi dũka daga gare su ga dukkan yãtsu ( 2 ) . »
13. Wancan ne, dõmin lalle ne sũ, sunã sãɓa wa Allah da ManzonSa. Kuma wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
14. Wancan ne: « Ku ɗanɗane shi, kuma lalle ne akwai azãbar wuta ga kãfirai. »
15. Yã kũ wacɗanda suka yiĩmãni! Idan kun haɗu da waɗanda suka kãfirta ga yãƙi, to, kada ku jũya musu bãyayyakinku.
16. Kuma duka wanda ( 3 ) ya jũya musu bãyansa a yinin nan, fãce wanda ya karkata dõmin kõɗayya, kõ kuwa wanda ya jẽ dõmin haɗuwa da wata ƙungiya, to, lalle ne ya kõma da fushi daga Allah, kuma matattararsa Jahannama, kuma tir da makõma ita!
( 1 ) A lõkacin zãfi ne na bazara,kuma aka faralta azumi, sai Allah Ya saukar da ruwa daidai da sansanin Musulmi, suka shã, suka yi wanka sa'an nan kuma aka daddale musu rairayi dõmin sauƙin tafiya.
( 2 ) Sa'an nan kuma Annabi da umurnin Allah ya ɗẽbi tsakuwa da hannunsa mai daraja ya jẽfa a jihar kãfirai. Bãbu wanda ya rage a cikinsu, fãce tsakuwar nan tã shiga acikin idãnunsa.
( 3 ) Gudu a wurin yãƙin Jihãdi shĩ ne mafi girman haram duka, matuƙar kãfirai ba su fi ninki biyu na adadin Musulmi ba, kamar yadda zai zo. Wanda ya yi gudu a wurin jihãdi kamar yã nẽmi kãfirci ya rinjãyi Musulunci ne.